Accessibility links

Breaking News

Batun Maido Da Zaman Lafiya Da Adalci a Sudan


Sharhin Muryar Amurka na wannan karon ya mai da hankali ne kan kokarin da masu ruwa da tsaki ke yi na maido da kwanciyar hankali a Sudan

Tun bayan da sojoji suka kwace mulki a Sudan a watan Oktoba, al'ummar Sudan suka rika cika tituna don neman kyakkyawar makoma ta yadda za su iya cimma burinsu na tabbatar da dimokuradiyya da mutunta hakkin bil'adama, in ji Ambasada Richard Mills, mataimakin wakilin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya a ranar 23 ga watan Agusta.

Amurka ta yi imanin cewa, " warware rikicin siyasar Sudan zai bukaci kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin farar hula da za ta iya yin aiki don cika alkawuran juyin juya halin 2019," in ji Ambassador Mills.

Ƙoƙarin haɗin kai na kasa da kasa na da mahimmanci don taimakawa wajen sauƙaƙe tattaunawar da Sudan ta jagoranta don maido da mulkin demokradiyya na Sudan da mulkin farar hula. Ambasada Mills ya ce "Za mu ci gaba da tallafa wa tawagar hadin gwiwa ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, ko UNITAMS, wajen aiwatar da aikinta, gami da tallafa wa yarjejeniyar zaman lafiya ta Juba."

Ya kara da cewa, "Muna ci gaba da firgita sanadiyyar tashin hankalin Darfur, wanda ya raba mutane sama da 100,000 da muhallansu. Rikicin tsakanin al'umma yana barazana ga hadin kan al'umma kuma yana rage yiwuwar zaman lafiya da dorewar tsarin zaman lafiya." Akwai matukar bukatar kare fararen hula, haka nan gyare-gyare a fannin tsaro, da kafa hanyoyin sa ido da bayar da rahoto na kasa da kasa.

Ambasada Mills ya taya kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Juba murnar samar da horo da kuma kafa rundunar hadin gwiwa ta tsaro ta Darfuri. "Wannan wani muhimmin mataki ne na inganta tsaron fararen hula," in ji shi.

Mai shigar da kara na kotun kasa da kasa ta hukunta manyan laifukan yaki a kasar Sudan ya bayyana a wani rahoto na baya bayan nan cewa mahukuntan Sudan sun dauki matakin bayar da taimako ga binciken da suke gudanarwa a yankin Darfur. Ambasada Mills ya bukaci irin wannan hadin kai da a ci gaba da yinsa. Sakamakon kokarin kotun, a watan Afrilu, Amurka ta yi marhabin da fara shari'ar Ali Mohammed Ali Abd-al Rahman, tsohon kwamandan Janjaweed da ke fuskantar tuhume-tuhume 31 na laifukan yaki da cin zarafin bil'adama.

A cikin watanni da dama da suka gabata, da yawa daga cikin shaidun sun yi tafiya na dubban mila-milai zuwa Hague don ba da labarin yadda ake kashe fararen hula, sata, cin zarafi, da wargaza al'ummomi a Darfur.

Amurka ta bukaci mahukuntan Sudan da su ci gaba da ba da hadin kai ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta hanyar ba da shaida da samun damar isa ga manyan shedu ba tare da wani cikas ba. Ambasada Mills ya jaddada cewa "Wadanda ke da sammacin kamawa daga kotun ICC dole ne su fuskanci shari'a kuma a mika su gaban kotu."

Amurka tana goyon bayan al'ummar Sudan a kokarinsu na tabbatar da dimokuradiyya, mai mutunta hakkin dan Adam, da wadata kasar Sudan.

Anncr: Wannan sharhi ne da ke bayyana ra'ayoyin Gwamnatin Amurka

XS
SM
MD
LG