Sakatare Blinken ya bayyana karara cewa, Amurka za ta ci gaba da ba da goyon baya wajen samun bayanai da kuma kare 'yancin 'yan jarida a duniya.
Amurka ta himmatu wajen yaki da ayyukan cin hanci da rashawa da kuma dabbaka tsarin Dimokradiyya, da bin doka a tsakiyar yankin Amurka.
"Samun makoma mai kyau abu ne mai yiwuwa," in ji ta. Amma yana buƙatar dukkan 'yan siyasa su yi watsi da ayyukan da ke haddasa rarrabuwar kawuna da maganganu masu tayar da hankali" In ji Power.
Amurka za ta ci gaba da zama mai ba da shawara ga al'ummar Venezuela yayin da suke kokarin ganin an maido da mulkin dimokradiyya cikin lumana ta hanyar zabe mai inganci da adalci.
Tun bayan juyin mulki, gwamnatin Burma ta daure mutum 10,000 sannan kuma aka kashe akalla 1,300 ciki har da kananan yara da dama.
"Dole ne mu yi amfani tsarin diflomasiyya na duniya don kawo karshen wadannan rikice-rikice," a cewar Power.
"Ya kamata mu ci gaba da jajircewa da hada kai a duniya baki daya a cikin watanni masu zuwa, yayin da muke ci gaba da yin aiki tuƙuru don kawo ƙarshen wannan annoba."
"Za mu ci gaba da yin amfani da dukkan karfin ikon Amurka wajen kai hari ga 'yan ta'addan da ke shirya ayyukan kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, da wadanda ke ba da damar, sauƙaƙewa, da kuma ba da kuɗin ayyukansu."
“Irin mummunan tasirin da sauyin yanayi ke yi, abu ne da ake gani a bayyane a sassan nahiyar – yunwa, sare dazuzzuka, rashin amfanin gona, ambaliya, kwararar hamada, rashin abinci, gasa don neman albarkatu, rugujewar tattalin arziki da ƙaura."
Load more