Accessibility links

Breaking News

Barazanar Da Ke Tattare Da ‘Yancin Walwalar Addini A Sassan Duniya


Blinken yayin da ayke jawabi kan 'yancin walwalar addini
Blinken yayin da ayke jawabi kan 'yancin walwalar addini

'Yancin walwalar addini na ci gaba da fuskantar barazana ga miliyoyin mutane a sassan duniya, in ji Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken

Yayin gabatar da sabon rahoton Amurka game da matsayin 'yancin walwalar addini na duniya, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce manufarsa ita ce ci gaba da bayyana manufofin Amurka "inda kowa zai iya zaɓa da aiwatar da addininsa:"

“Mutunta ’yancin walwalar addini yana ƙarfafa wasu haƙƙoƙi, kamar ’yancin yin magana ba tare da fargaba ba, yin taro cikin lumana, da ikon shiga da sa hannu a sha’anin siyasa. Kare wannan haƙƙi na duniya yana ba mutane damar bayyana ra'ayoyinsu, su rayu gwargwadon ƙarfinsu, don ba da gudummawa sosai ga al'ummominsu. "

Amma duk da haka a yau, 'yancin walwalar addini na ci gaba da fuskantar barazana ga miliyoyi, in ji Sakatare Blinken:

“Cibiyar Bincike ta Pew a kwanan nan, ta gano cewa takunkumin gwamnati a kan addini ya kai matakin da ya fi girma a duniya tun lokacin da aka fara bin diddigi a shekara ta 2007. A yau gwamnatoci a fadin duniya na ci gaba da hantarar mutane, nuna matsin lamba ga wuraren ibada, kuma suna daure mutane saboda imaninsu.”

A cewar Blinken, wasu kasashen suna tauye hakkin wasu nau'ukan tufafin addini; wasu kuma sun sanya shi wajibi ne. Wasu gwamnatoci suna kai wa ga iyakokinsu don kai wa mutane hari saboda imaninsu ko tallata ‘yancin walwalar addini.

“A kowane yanki, mutane suna ci gaba da fuskantar tashin hankali da ke da nasaba da addini, ana nuna musu wariya, daga gwamnatoci da kuma ’yan’uwansu. Za a iya hana su zuwa makarantu, hana su aikin yi, muzgunawa, duka, ko wani abin da ya fi muni."

Kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi kuma suna kai hari kan mutane bisa addininsu. Sakatare Blinken ya yi nuni da harin da aka kai a watan Yuni a coci-coci da majami'a a yankin Dagestan na kasar Rasha inda aka kashe 'yan sanda da farar hula da wani limamin coci. Ya ce tun bayan harin ta'addancin da Hamas ta kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma rikicin da ya biyo baya a Gaza, matsalar nuna kyama ga Yahudwa da Musulmi ta karu sosai a fadin duniya.

Rubuce-rubucen kan irin wannan cin zarafi, tsayin daka kan yaki da nuna ƙiyayya da zalunci, kare haƙƙin ‘yancin addini ga kowane mutum, sune kan gaba a manufofin Amurka na ketare.

Sakatare Blinken ya ce, "a ƙarshe, wannan aikin yana game da kare wani muhimmin sashe na abin da ake nufi da zama ɗan adam: ikon gano wani abu mafi girma fiye da kanmu.

Haƙƙin zaɓin abin da muka yi imani kuma yana ba mu damar koyi daga waɗanda suka bambanta da mu, kuma mu yi bikin duk abin da muke da shi.

Da yake ambato ƙaulin ƙwararren masani na addini na Houston Smith, Sakatare Blinken ya ce, “‘Idan muka ɗauki addinan da ke dawwama a duniya da kyau, za mu gano hikimar da ke tattare dan Adam.”

Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayin Gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG