Accessibility links

Breaking News

Bukatar Gaggauta Kama Tafarkin Zaman Lafiya a Yankunan Great Lakes Na Afurka.


Rikicin Kasashen Yankin Tafkin Great Lakes
Rikicin Kasashen Yankin Tafkin Great Lakes

Sake dawo da fadan da aka yi a watan Oktoba a lardunan Gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, ya wargaza wata ‘yar lumanar tsawon watanni shida: ‘yar kwarya kwaryar lumana ta tsawon watanni shida wadda, a cewar Majalisar Dinkin Duniya, "ba ta inganta komai ba a kasar, sabanin yadda aka zata" a kan "tsaro ko matakan jinkai." Tabbas, "hadarin yin arangama kai tsaye tsakanin DRC da Ruwanda, wadanda ke ci gaba da zargin juna da tallafa wa kungiyoyi masu dauke da makamai… na gaske ne."

Dawo da fadan dai dorawa ne kan karo na biyu na boren watan Oktoban bara na kungiyar M23, wadda ta kunshi galibin 'yan kabilar Tutsi daga makwabciyarta Rwanda, da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai. Mafi yawa suna sha'awar hako albarkatun ma'adinan Kongo ba bisa ka'ida ba, kodayake M23 kuma na ikirarin kare 'yan Tutsi da ke zaune a DRC.

Wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta ce "Halin tsaro a yankin Great Lakes na ci gaba da tabarbarewa yayin da rikici tsakanin DRC da Rwanda ke kara tsanani."

“Na sake maimaita kiranmu ga Rwanda da ta gaggauta kawo karshen goyon bayan da take bai wa kungiyar M23 da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa takunkumi ta kuma janye daga yankin DRC. Muna kuma kira ga FARDC da ta yanke hulda da FDLR da Majalisar Dinkin Duniya ta ki amincewa da ita."

Kazalika, "Muna kira ga sojojin yankin da aka tura zuwa gabashin DRC, ko ta bangaren biyu ko kuma ta yankin Gabashin Afrika, da su hada kai da juna da kuma [Tawagar tabbatar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo," in ji jakadiya Thomas-Greenfield. "Kuma dole ne su… su guje wa take hakkin dan adam da cin zarafi da ayyukan haram, gami da hakar ma'adinai na haram."

“Saboda rashin zaman lafiya a yankin, al’amuran jinkai sun tabarbare har zuwa wani mataki mai ban tsoro. Rikici ya raba mutane fiye da rabin miliyan da muhallansu a shekarar 2023 kadai, da yawa daga cikinsu ana tilasta musu rayuwa ba tare da samun isasshen abinci, ruwa, ko kula da lafiya ba a sansanonin da suka cika fiye da kima."

"Rashin kwanciyar hankali na siyasa ya sukurkuta harkar samar da abinci da rarrabawa, wanda ya haifar da karancin abinci," in ji Ambasada Thomas-Greenfield.

“Mutane miliyan 1.5 na fuskantar matsalar karancin abinci na gaggawa, kuma hakan ba zai yiwu ba a karni na ashirin da daya. Rikicin siyasa da mutum ya haifar ya zama rikicin jinkai da mutum, kuma dole ne a kawo karshensa.”

Ambasada Thomas- Greenfield ta ce "Ina kira ga shugabannin yankin da su ci gaba da tattaunawa a bude, musamman yayin da zabukan kasa na DRC ke gabatowa." “Dole ne wadannan zabukan su kasance masu gaskiya da adalci ga kowa, gami da mata da kananan kabilu. Dukkanin fararen hular Kongo sun cancanci yancin rayuwa cikin lumana, da kuma jin muryarsu a rumfunan zabe."

Anncr: Sharhin Muryar Amurka kenan mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG