Accessibility links

Breaking News

NATO TA SHA ALWASHIN TAIMAKA MA UKRAINE


Blinken
Blinken

Anncr: Yanzu kuma sai sharhin Muryar Amurka, mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka:

Idan har akwai wata babbar nasara guda da aka samu daga taron ministocin harkokin wajen kasashen NATO na baya-baya nan da aka yi a Brussels na kasar Belgium, ita ce dorewar goyon bayan da kawancen ke da shi ga Ukraine, in ji Sakataran Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken.

Blinken ya kara da cewa, “Wasu na tambayar ko Amurka da sauran abokan kawancen NATO za su ci gaba da mara baya ga Ukraine yayin da muke shiga lokacin hunturu a karo na biyu na zalincin Putin. Amma amsar a nan, NATO, a fili ta ke kuma babu tantama. Ya zama wajibi a gare mu, kuma za mu ci gaba da tallafa wa Ukraine. Tabbatar da cewa yakin mamayar da Rasha ta kaddamar bai sami nasara ba. Yana da matukar muhimmanci a yau, kamar lokacin da Kremlin ta kaddamar da yakin kusan shekaru biyu da suka wuce.”

Sakatare Blinken ya ce “Bana jin wata alamar gajiyawa ko ja da baya, akasin haka, akwai kwarin gwiwa don ci gaba da matsa lamba.” “Kuma akwai dalili mai kyau akan hakan. Ya kara da cewa “Ina ganin dukkan abokan kawancen sun gano cewa wannan batu ne ba kawai na yin abin da ya dace ba, batu ne na muradun kai, ciki har da na Amurka.”

Ya ci gaba da cewa, “Idan muka kyale wata kasa kamar Rasha ta ci karen ta babu babbaka don sake fasalin iyakokin wata kasa da karfi, don kokarin yin karfa-karfa kan makomar wata kasa, idan hakan ya faru ba tare da wani hukunci ba, to an bude kofa ga kuma duk wani mai kokarin yin zalinci da danniya a ko’ina da zai iya daukar darasi daga hakan. Wannan shine dalilin da ya sa yake da muhimmanci a garemu, har ma ga kowace kasa, mu tsaya tsayin daka ga Ukraine.”

Sama da kasashe 50, ciki har da akasarin mambobin kungiyar tsaro ta NATO, sun kuduri aniyar tabbatar da cewa Ukraine “ta na da duk abin da take bukata, ba kawai don kare kanta daga hare-haren Rasha ba, haka ma don taimaka mata ta sake kwato yankunan da Rasha ta kwace mata,” abin da Sakatare Blinken ya jaddada kenan.

Ya ci gaba da cewa, “Har ila yau, kuma ina ganin wannan yana da matukar muhimmanci, alkawarin da wasu kasashe su ka yi na taimaka wa Ukraine wajen gina wata runduna nan gaba, wacce za ta iya tabbatar da hana kai hari da kuma tabbatar da kariya daga mamaya a nan gaba.”

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi imanin cewa ko ta yaya zai iya ci gaba da mamaye Ukraine, al’ummarta da magoya bayanta, in ji Sakatare Blinken. “Ayyukan kungiyar kawancen NATO, ayyukan daidaikun kasashen da ke cikin wannan kawancen da ma sauran kasashe da dama na duniya shi ne karfafa Ukraine, don taimaka mata wajen kare kanta, da kuma daidaita makomarta, wannan ita ce hanya daya tilo da ta fi dacewa wajen kawar da wannan mummunan tunani na Putin.”

Anncr: Wannan ne Muryar Amurka mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG