Accessibility links

Breaking News

Wani Abin Tashin Hankali A Ukraine


Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken

A matsayinta na mamba a yarjejeniyar da aka cimma a Geneva, akwai nauyi da ya rataya a wuyan Rasha na kada ta kai hari kan muhimman kayayyaki da suke da “hadari, ciki har da madatsar ruwa” musamman idan wannan hari zai haifar da illa ga fararen hula.

A ranar 6 ga watan Yuni, an kassara Madatsar ruwan Karkhovka da ke yankin Kharson a Ukraine tare da lalata tashar samar da makamashi.

Dakarun Rasha ne suka karbe ikon madatsar ruwan bayan da suka mamaye Ukraine kuma har yanzu yana karkashin ikonsu.

Ko da yake, babu tabbacin ko wani abu ne ya lalace ko kuma batawa aka yi da gangan, wani abu shi ne, babu haufi fashewar madatsar ruwan ba za ta auku ba idan da dakarun Rasha ba su kai hari ba.

“Rasha ce ta fara wannan yaki, ita ce ta karbe ikon wannan yanki na Ukraine, kuma su ne suka karbe ikon madatsar ruwan ba bisa ka’ida ba a shekarar da ta gabata, kuma lokacin suke rike da wurin,” in ji wakilin Amurka na musamman kan sha’anin siyasa, Robert Wood.

Hare-haren na gangan da ake kai wa fararen hula, abu ne da aka haramta a dokokin yaki.

A matsayinta na mamba a yarjejeniyar da aka cimma a Geneva, akwai nauyi da ya rataya a wuyan Rasha na kada ta kai hari kan muhimman kayayyaki da suke da “hadari, ciki har da madatsar ruwa” musamman idan wannan hari zai haifar da illa ga fararen hula.

Babu shakka, kamar yadda Karamin Sakatare Janar mai kula da sha’anin ayyukan jin-kai da ba da taimakon gaggawa Martin Griffiths ya ce, lalata madatsar ruwan Kakhovka, na daya daga cikin muhimman hadurra da suka lalata ababen more rayuwar fararen hula, tun da Rasha ta mamaye Ukraine.

Bugu da kari, “lalata madatsar ruwan, ya kara sa samar da wutar lantarki ya zama abu mai wuya, wanda hakan, zai iya haifar da wasu matsaloli a yankin tashar nukiliyar Zaporizhzhya, in Ambasada Wood.

“Ya zama wajibi, sashen da ke sanyaya tashar nukiliya ta Zaporizhzhya, wanda ke janyo ruwa daga madatsar ruwan, ya kasance a cikin yanayi mai kyau domin aikin sanyaya tashar nukiliyar da yake yi. Muna kira ga Rasha da ta mayar da sashen da ke aike wa da bayanai ga fararen hula masu kula da wannan bangare ta kuma bar hukumar da ke takaita mallakar makaman nukiliya ta IAEA ta samu bayanai na Hakika kan duk wani abu da ke faruwa a yankin tashar nukiliyar.

“Amurka za ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashen duniya wajen ganin an dola alhkin duk wani ta’asa da ta aikata akanta. Za mu ci gaba da nuna goyon bayan ga Ukraine don ta kare kanta daga muguntar fadar Kremlin. In ji Amabasada Wood.

Ya kara da cewa, “hanya mafita a bayyane take: ya zama wajibi Rasha ta janye dakarunta daga Ukraine. Sannan wajibi ne kuma ta kawo karshen wannan yaki tare da kawo karshen kangin wahala da ta jefa mutane a ciki.”

Sanarwa: Wannan shi ne sharhin Amurka ne da ke bayyana ra’ayin gwamnatin kasar.

XS
SM
MD
LG