Accessibility links

Breaking News

Kawancen Yankin Atlantika Gawurtacce Ne


Antony Blinken
Antony Blinken

Ga sharhin Muryar Amurka, mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka

Kwanan nan Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya gana a Brussels da shugabannin kasashen Turai da dama a tarurrukan da suka jaddada mahimmanci da kuzarin kawancen kasashen yankunan ketaren Atlantic.

Bayan wata ganawa da babban wakilin kungiyar EU mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro Josep Borrell, Sakatare Blinken ya ce tattaunawar tasu ta hada da kalubalen duniya inda hadin gwiwar Amurka da Turai zai iya kawo sauyi, kama daga Habasha zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya zuwa Gabas ta Tsakiya.

To amma, abin da suka fi mayar da hankali a kai, shi ne yaki iri na takala da Rasha ta kai ma Ukraine.

Sakatare Blinken ya ce "Amurka da EU na ci gaba da aiki a cikin wasu kulle-kulle, tare da wasu kawancen abokan hadin gwiwa… don tabbatar da cewa Ukraine za ta iya kare kanta, jama'arta, yankinta, 'yancin zabar hanyarta," in ji Sakatare Blinken.

Ya yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu, abokan Amurka na tarayyar turai sun kashe kimanin dalar Amurka biliyan 13 wajen taimakon soji ga kasar Ukraine, baya ga tallafin tattalin arziki da na jinkai na biliyoyin daloli. Bugu da kari, kwanan nan kungiyar EU ta sanar da cewa za ta baiwa Ukraine karin harsashi na Euro biliyan 2 ta hanyar Cibiyar Zaman Lafiya ta Turai. Har ila yau, Amurka ta sanar da wani sabon taimakon soja ga Ukraine wanda ya hada da harsasai da kayan aiki na dalar Amurka miliyan 500, da harsasai na dala biliyan 2.1, da rokoki, da makaman tarwatsa kayan sulke da sauransu.

Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka suna kuma "kakaba tsauraran takunkuma da sa ido kan kayakin da ake fitarwa ta yadda zasu rage karfin Rasha na iya yaki," in ji Sakatare Blinken.

Ya yaba wa kungiyar Tarayyar Turai da ta yanke dogaro da iskar gas ta Rasha daga kusan kashi 40 cikin dari a farkon yakin zuwa kusan kashi 15 a karshen shekarar 2022 - tare da taimakon karuwar kashi 140 cikin 100 na iskar gas da Amurka ta fitar zuwa Turai a bara.

Wani fanni na hadin gwiwa irin wanda ba a taba gani ba shi ne tabbatar da wanzuwar makamashi, wanda ke bukatar sadaukar da kai don hana aukuwar matsalar yanayi. Amurka da EU, a cewar Sakatare Blinken, sun kuduri aniyar gaggauta karkata ga amfani da makamashi mai tsafta a duniya, habbaka hanyoyin samar da makamashi masu aka akai masu jimiri, kuma lafiyayyu.

Sakatare Blinken ya lura cewa gudanar da dukkan tattaunawar da babban wakili Borrell ya kasance tare da haɗin gwiwa don farfado da dimokuradiyya da dabi'un dimokuradiyya.

Sakatare Blinken ya ce, "Dangantaka tsakanin Amurka da Tarayyar Turai ita ce mafi tsari, it ace dangantaka mai karfi a duniya," in ji Sakatare Blinken. Ya kara da cewa, "kuma na ji dadin… ci gaba da gudanar da aiki da ingantaciyar rayuwa ga mutane a kowane bangare na Tekun Atlantika."

Wannan shine sharhi kan ra’ayoyin gwamnatin Amurka

XS
SM
MD
LG