Accessibility links

Breaking News

Don Ganin Tsarin Dimokaradiyya Ya Amfanar


USA-BIDEN/DEMOCRACY
USA-BIDEN/DEMOCRACY

A cikin watan Maris, an gudanar da taron koli na Dimokuradiyya na biyu ta yanar gizo a birnin Washington, D.C. da wasu garuruwa da dama da suka yi hadin gwiwa wurin karbar bakuncin taron, da ya tattaro shugabanni da wakilan kasashe fiye da dari, da kuma abokan hulda daga kungiyoyin farar hula da masu zaman kansu.

A yayin jawabin rufe taron, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce duniya ta kai wata gabar sauyi game da makomar dimokuradiyya - "ko muna son yin abin da ake bukata don tabbatar da cewa dimokuradiyya ta ci gaba da isa ga jama'arsu."

A cikin shekarar da ta gabata da aka gudanar da ayyuka tun bayan taron kolin Dimokuradiyya na farko, ya ce, “Wannan kungiyar ta amsa wannan tambayar da babbar murya.. .” Mun yi – kuma mun cika – fiye da alkawura 700 da ke taimaka mana wajen kariya da karfafa manufofi da cibiyoyin dimokuradiyya.”

Sakatare Blinken ya yi nuni da wani misali, ga sabbin dokoki da tsare-tsare na yakar cin hanci da rashawa da Ecuador, Dominican Republic, da Australia suka dauka; matakan tallafawa walwala da ‘yancin 'yan jarida da Faransa, Slovakia, New Zealand da Amurka suka dauka ta hanyar shirye-shiryen da ke taimakawa ‘yancin kafafen yada labarai su sami karfin tattalin arziki; ga soke dokokin, kamar yadda ake yi a Zambiya, wadanda za a iya amfani da su don rufe bakin masu sukar gwamnati; da kuma ayyuka don kare hakkin al’umma da na dan adam, ciki har da na ‘yaan asalin kasar da wadanda ke cikin al'ummar ludu da madigo (LGBTQI+).

Sakatare Blinken ya ce, "Yayin da muke shirye-shiryen tarurruka masu zuwa, za mu ci gaba da taimakon juna, da dorewa, da daidaitawa, da kuma karfafa kokarinmu na hadin gwiwa."

Sakatare Blinken ya ayyana cewa "Lallai hakan ne ya sa, muka yi aiki tare don kawo irin wannan gungun masu halartar taron kolin don samar da ci gaba a kan abubuwan da muka sa gaba - daga inganta ayyukan matasa a cikin siyasa, tallafawa ‘yancin 'yan jarida, tabbatar da zabe na gaskiya da adalci da kuma tsara ka'idoji dake tattare da yanar sadarwa da fasahohi masu tasowa."

Sakatare Blinken ya ce, "Ba mu yi imani cewa muna rike dukkan mafita ba – ko kadan. Amma mun san cewa idan muka hada kai da ’yan uwanmu na dimokuradiyya, muna kara wa juna karfi, da jajircewa, da taimakawa ’yan kasar mu, da kuma iya aikata abin da ya tara mu nan, wato isar da su – , Ina kyakkyawar fata ga duniya."

Wannan shine sharhin Muryar Amurka da ya bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG