Accessibility links

Breaking News

Amurka Na Kira Ga Majalisar Lafiya Ta Duniya Da Ta Gayyaci Taiwan A Matsayin 'Yar Kallo


Antony Blinken
Antony Blinken

Ga Sharhin Muryar Amurka Mai Bayyana Ra’ayin Gwamnatin Amurka.

Majalisar Koli Ta Lafiya ta kasa da kasa, WHA a takaice, gamayya ce ta kungiyoyin lafiya da ke karkashin Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO, wace ta ke da alhakin bada shawarwari. Kungiyar tana shirin gudanar da taron kolinta na shekara-shekara daga ranar 21-30 ga watan Mayu mai ci a Geneva.

Taken burin WHO shi ne, “samar wa kowa lafiya” sannan kamar yadda sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce, a wata sanarwa kafin taron, taron WHA na shekara shekara wata dama ce ta musamman ga wakilan lafiya da kwararru daga sassan duniya baki daya su taimaka wajen ciyar da harkar lafiyar duniya gaba da tsaron lafiyar duniya.

La’akari da manufar taron, Sakatare Blinken ya karfafa gwiwar WHO “matuka” ta gayyato Taiwan a matsayin mai sa ido a taron majalisar kolin na bana domin ta bada gudunmawarta akan kwarewarta a tattaunawar da za ayi.

Babu tantama a game da kwarewar Taiwan a bangaren lafiyar duniya, kazalika bajintarta a bangaren kimiya, iya mulkin demokradiyya, jajircewarta akan COVID-19 da kuma tattalin arzikinta mai bunkasa, dukkaninsu al’amuran da za su iya tasiri ne a tattaunawar majalisin WHA.

Bugu da kari kuma, gayyato Taiwan a matsayin mai sa ido zai bayyana jajircewar WHO wajen tabbatar wa kungiyoyin lafiyar duniya matakan “Samarwa Kowa Lafiya” a cewar Sakatare Blinken, ya kuma bayyana cewa, an gayyaci Taiwan a matsayin mai sa ido a tarukan WHA a baya.

Hasali ma dai, WHO ta saba abin da ta saba yi shekara da shekaru a shekarar 2015 wajen taron majalisin lafiya na duniya karo na 70, da ta gaza gayyato wakilan Taiwan zuwa taron a matsayin mai sa ido-gazawar da aka ci gaba da maimaitawa kowace shekara daga wannan lokaci.

“Ware Taiwan daga taron majalisin lafiyar duniyar ta WHA, majalisin dake jagorantar al’amuran cigaba a fannin lafiyar duniya, wani al’amari ne da ba shi da hujja kana yake raunana samun hadin kai agame da lafiyar al’ummar duniya da tsaro, wanda duniyar take bukata,” a cewar Sakatare Blinken.

Blinken y ace “Taiwan amintacciyar abokiyar tarayya ce mai tsarin demokradiyya mai nagarta kana wata madogara ce mai kyau a duniya.” Ya kara da cewa, “Amurka zata ci gaba da kokarin ganin cewa Taiwan ta dawo matsayinta na mai sa ido a majalisin WHA, bugu da kari kuma, domin gudunmawar ta mai fadi akan al’amuran da suka dace a zauruka na fadin duniya.

“Goyon bayanmu kan Taiwan ta hallarci tarukan da suka dace na kasa da kasa”, a cewar Blinken, yana da nasaba da kudurinmu na China-Guda, wanda yake la’akari da dokar mu’amalar Taiwan, sanarwar hadin gwiwar Amurka da China uku da kuma tabbaci daidai har shida (three U.S.-China Joint Communiques, and the Six Assurances).

Wannan shi ne sharhin Muryar Amurka mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG