Accessibility links

Breaking News

Bayanin Harris Kan Batun Fadada Dangantakar Amurka Da Zambiya


USA-AFRICA/HARRIS-ZAMBIA
USA-AFRICA/HARRIS-ZAMBIA

Yanzu kuma sai sharhin Muryar Amurka wanda zai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.

Mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta gana da shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema a ziyarar da ta kai nahiyar Afirka. Shugabannin biyu sun tabbatar da aniyarsu ta ciyar da dimokuradiyya gaba a kasar Zambiya da ma duniya baki daya, kuma mataimakiyar shugaban kasar ta sanar da sabbin tsare-tsare na dimokuradiyya don inganta yaki da cin hanci da rashawa, gyare-gyaren harkokin mulki, da kuma nuna gaskiya a fannin kudi a kasar ta Zambia.

Ta ce, “Hakika kasar Zambiya ta fara wani gagarumin shiri na kawo sauyi a tsarin dimokuradiyya a karkashin jagorancinka, mai girma shugaban kasa. Kuma kamar yadda na sha fada a baya kan wannan tafiya, dimokuradiyya da shugabanci nagari a duniya abu ne da Amurka ta sa gaba, kuma za mu tsaya tare da masu fafutukar tabbatar da wadannan ka'idoji. Don haka, na yi farin cikin sanar da sama da dala miliyan 16 don samar da sabbin shirye-shirye a Zambiya, tare da maida hankali kan yaki da cin hanci da rashawa da sauran kokarin kawo sauyi.

Mataimakiyar shugaban kasar Harris ta bayyana cewa, Amurka ta kuduri aniyar tura karin kamfanoni masu zuba jari masu zaman kansu zuwa kasar Zambiya da ma nahiyar Afirka don kara habaka kirkire-kirkire da harkokin kasuwanci da aka riga aka fara.

Ta ce, "Don karfafa dangantakar kasuwanci, ina farin cikin sanar da cewa Amurka da Zambia za su rattaba hannu kan wata yarjejeniyar ci gaban kasuwanci - yarjejeniyar fahimtar juna - wadda zata taimaka wajen bunkasa da aiwatar da ayyukan kasuwanci da kuma kara yawan kayayyaki da ayyuka tsakanin kasashenmu.

Mataimakiyar shugaban kasar ta kuma tabbatar da kudurin Amurka na farfado da tattalin arzikin kasar Zambia tare da maraba da ajandar sake fasalin tattalin arziki na shugaba Hichilema. Ta baiwa shugaba Hichilema tabbacin cewa Amurka ta dauki matakin kammala duban batun basussukan Zambia a matsayin babban fifiko:

Ta ci gaba da cewa, "Za mu ci gaba da kasancewa abokan hadin gwiwa mai karfi don habbaka tattalin arziki na dogon lokaci da bunkasa zuba jari a Zambia. Kuma za mu ci gaba da bayar da shawarwari don gaggauta kammala aiki kan basussukan Zambiya da kuma sake fasalin bashin...Gwamnatinmu ta yi imanin cewa, akwai bukatar kasashen duniya su taimakawa kasashe irin su Zambia su dawo da martabarsu. Don haka, zan sake nanata kiran da muka yi sau da yawa ga duk masu ba da lamuni don samar da rage bashi mai ma'ana ga Zambia.

Shugabannin biyu sun kuma tattauna batun hadin gwiwa a Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar raya kasashen kudancin Afirka, ciki har da batun rashin tsaro a yankin.

Amurka na fatan fadada alakar dimokuradiyya, tattalin arziki, da huldar muhalli da kasar Zambiya a shekaru masu zuwa.

Wannan shine sharhin Muryar Amurka wanda ya bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka .

XS
SM
MD
LG