Accessibility links

Breaking News

Fafutukar Kare Hakkin Bil Adama Da Tsaro A Kenya


'Yan sandan kwantar da tarzoma a birnin Nairobi da ke Kenya, on Yuli 2, 2024
'Yan sandan kwantar da tarzoma a birnin Nairobi da ke Kenya, on Yuli 2, 2024

Amurka ta kuduri aniyar yin aiki kafada da kafada da gwamnati da jama'ar Kenya yayin da suke kokarin magance kalubalen tattalin arzikinsu, tare da tabbatar da kare hakkin bil'adama a Kenya da ma duniya baki daya.

Amurka tana ba da shawarar tabbatar da kariya da tsaro a Kenya. An gudanar da gagarumar zanga-zanga a babban birnin Nairobi bayan da aka gabatar da kudirin dokar kudi da zai kara haraji a kasar.

An sami "rahotanni cin zarafin masu zanga-zanga" in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller yayin wani taron manema labarai. Amurka ta yi kira ga gwamnatin Kenya da ta yi amfani da hanyoyin lumana tare da hana cutar da fararen hula wajen tunkarar zanga-zangar lumana.

“Don haka, muna Allah wadai da tashin hankalin da aka ba da rahoto a lokacin zanga-zangar da aka yi a Nairobi da kuma kewayen Kenya. Muna jimamin asarar rayuka da jikkata da aka samu tare da yin ta'aziyya ga iyalan da suka rasa 'yan uwansu. Muna rokon a dage don maido da tsari da samar da sarari don tattaunawa."

Tuni dai shugaban kasar Kenya William Ruto ya janye dokar harajin. A wata rubutacciyar sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fitar, ya godewa shugaba Ruto bisa daukar matakan rage zaman dar-dar da kuma yin alkawarin zaman tattaunawa da masu zanga-zangar da kungiyoyin farar hula.

Sakatare Blinken ya jaddada muhimmancin jami’an tsaro kan gujewa amfani da karfin tuwo a kuma gudanar da bincike cikin gaggawa kan zarge-zargen cin zarafin bil’adama.

Har ila yau, Kenya ta taka rawar gani wajen ba da gudunmawar rundunar wanzar da zaman lafiya ga Tawagar Taimakon Tsaro na Kasa da Kasa da nufin maido da tsaro da wadata a Haiti. Kakakin Miller ya jaddada cewa, dukkan ma'aikatan da suka hada da Kenya da sauran kasashe suna samun horo mai zurfi kan hakkin ‘dan adam kafin a tura su.

Amurka ta sha yin aiki da Kenya da sauran abokan hulda wajen “daukan matakan karewa, da bincike da magance tare da sanar da jama’a rahoton da ya shafi take hakkin bil Adama karkashin shirin MSS,” a cewar Kakaki Miller.

“Za mu ci gaba da aiki da kwararrun ma’aikata da su saka hannu a wannan shiti, saboda hakan ya nuna yana da muhimmanci a mutunta hakkin bil Adama na al’umar Haiti domin maido da doka da oda."

Amurka ta kuduri aniyar yin aiki kafada da kafada da gwamnati da jama'ar Kenya yayin da suke kokarin magance kalubalen tattalin arzikinsu, tare da tabbatar da kare hakkin bil'adama a Kenya da ma duniya baki daya.

Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.


XS
SM
MD
LG