Accessibility links

Breaking News

Hana 'Yan Ta'adda Safarar Albarkatun Kasa


Linda Thomas-Greenfield
Linda Thomas-Greenfield

Yau sharhin Muryar Amurka mai bayyana ra'ayin Gwamnatin Amurka ya mai da hankali ne kan muhimmancin hana 'yan ta'adda da dangoginsu safarar albarkatun kasa.

Sanarwa: Yanzu kuma ga sharhin Muryar Amurka mai bayyana ra’ayin Gwamnatin Amurka.

Al’amarin ta'addanci da tsararrun manyan laifuka wani abu ne mai karfi a fadin Afirka, inda yake dada wanzuwa. A cewar Majalisar Dinkin Duniya, wadannan kungiyoyi, ta wani bangaren su na daukar nauyin ta wajen amfani da albarkatun kasa na yankunan da suka mamaye ba bisa ka'ida ba. Hakika, Ghada Waly, shugaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da miyagun kwayoyi da laifuffuka ya lura cewa akwai kyakkyawar shaida cewa yin amfani da karafa da ma'adanai masu daraja ba bisa ka'ida ba yana samar da kudade masu yawa ga masu tsattsauran ra'ayi. Har ila yau, fataucin namun daji shi ne tushen samun kuɗi mai dunbun yawa ga waɗannan ƙungiyoyi. Sana'ar hauren giwa ba bisa ka'ida ba kawai na kawo kusan dala miliyan dari hudu a duk shekara.

Idan ana so a dakile wadannan aika aika, dole ne a mai da hankali kan muhimman fannoni guda uku, in ji Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas Greenfield. "Na farko, a yanayi irin na Afirka, kasancewar mutane da kungiyoyi masu alaka da al-Qa'ida da ISIS na bukatar sa ido sosai da daukar mataki."

“Kudi na ci gaba da zama tushen rayuwar ‘yan ta’adda. Dole ne mu kara himma a kokarin da mu ke yi na daukar mataki nan masu bayar da kudi kai tsaye da masu taimakawa da hanyoyin samun kudi ga 'yan ta'adda da kungiyoyin ta'addanci. Kuma dole ne mu dakile mahimman hanyoyin samar da kudi waɗanda ke amfana da rashin ingancin matakan sa ido.”

"Na biyu, daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali da kuma kara kaimi a Afirka shi ne dabarun kungiyar Wagner da ke samun goyon bayan Rasha na yin amfani da albarkatun kasa na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Mali, da Sudan, da kuma sauran kasashe."

“Akwai cikakkun rubutattun bayanan wadannan abubuwan da ke faruwa kuma ba za a iya karyata su ba. Kuma mun san cewa ana amfani da waɗannan kudaden da ake samu ta munanan hanyoyi wajen karfafa yaƙe yaken da Rasha ke yi a Afirka, Gabas ta Tsakiya, da Ukraine. Kuma maimakon zama abokin aiki na gaskiya da inganta tsaro, kamfanin yaki na Wagner yana kwarar kasashen da ke biyansa da zinari, azurfa, katakai, da sauran albarkatu saboda ayyukan tsaro da ya ke yi masu ta hanyoyin rashin Imani. Wannan wani fanni ne na tsarin kasuwancin kamfanin Wagner."

A karshe, dole ne kasashe mambobin kungiyar ta NATO su kara kaimi wajen tunkarar al-Qa’ida, ISIS, da sauran kungiyoyin masu ta’addanci a Afirka. Takunkumin da aka kakaba wa gwamnatocin da suka amince da irin wadannan ayyuka ko ma su na da nasaba da yaki da safarar albarkatun kasa.

Ambasada Thomas Greenfield ta ce "Dukkanmu muna da alhakin magance haramtacciyar safarar albarkatun kasa a Afirka, wanda ya kai ga sace dukiyar jama'ar Afirka." “Yana da kyau mu hana masu fataucin yin amfani da miyagun ayyukansu da dukiyarsu ta haramtacciyar hanya wajen rura wutar rikici da ta’addanci. Kuma yana cikin ikonmu na hana lalata muhalli, bautar da yara, korar jama’a, take hakkin bil’adama da cin zarafi, da asarar kudaden shiga na gwamnati wanda hakan ya samo asali ne daga haramtacciyar safara.”

Sanarwa: Wannan shi ne sharhin Muryar Amura, mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG