Accessibility links

Breaking News

SHARHIN MURYAR AMURKA: Batun Jaddada ‘Yancin Labarai A Iran.


Zanga zanga kan mutuwar Mahsa Amini
Zanga zanga kan mutuwar Mahsa Amini

Sharhin Muryar Amurka, mai bayyana ra'ayin gwamnatin Amurka, wannan karon ya tabo batun zanga zangar da ake kan yi a Iran kan mutuwar budurwar nan mai suna Mahsa Amini

Gwamnatin Iran ta katse hanyar yanar sadarwa ga akasarin 'yan kasarta miliyan 80 don hana su da sauran jama’ar duniya ganin yadda ta ke mummunan murkushe masu zanga-zangar lumana sakamakon kisan gillar da aka yi ma Mahsa Amini a hannun 'Yan Sandan Tabbatar da Da’a na Iran.

"Mahsa Amini ta mutu sanadiyyar rashin hankalin wasu da kuma tsautsayi, kuma a yanzu gwamnati na murkushe masu zanga-zangar lumana da suka fusata game da rashinta da aka yi," in ji Sakataren Gwamnatin Amurka Antony Blinken. "A bayyane yake cewa gwamnatin Iran tana tsoron mutanenta."

Jami'an 'yan sandan Iran sun kama Malama Mahsa bisa zargin cewa ba ta sa hijabi daidai ba. Ta samu munanan raunuka yayin da take tsare kuma daga baya ta mutu a asibiti bayan da ta suma.

Rahotannin kafafen yada labarai na nuna cewa akalla mutane 76 ne aka kashe sannan sama da mutane 1,200 aka kama a fadin kasar ta Iran. Masu zanga-zangar na neman a kawo karshen tilasta sanya hijabi da kuma take hakkin mata a Iran. Zanga-zangar ta bazu zuwa akalla garuruwa 80 a fadin kasar.

Yayin da gwamnatin Iran ke ci gaba da luguden wuta kan masu zanga-zangar lumana tare da katse hanyoyin da al'ummarta ke samun amfani da kafar Intanet a duniya, Amurka na daukar matakin taimaka wa al'ummar Iran wajen samun bayanai ta yanar sadarwa cikin sauki.

Shi ya sa Ofishin Kula Da Kadarorin Kasashen Waje na Baitulmalin Amurka ya ba da Babban Lasisin D-2 – wanda wani fadadadden izini ne wanda zai ba wa kamfanonin fasahar sadarwa damar samar da karin sabis na ga mutane a Iran, kama daga samun damar yin amfani da rumbun ajiyar bayanai na Cloud zuwa ingantattun kayan aiki don inganta tsaronsu ta yanar sadarwa da kuma sirrinsu.

Wadannan matakan za su taimaka wa Iraniyawa wajen dakile yunkurin gwamnatin Iran na sa masu ido da kuma katse. Da wannan babban sabon lasisin, yanzu ya rage ga kamfanonin fasahar sadarwa su yanke shawara ko za su ba Iraniyawa sabis da aka halatta.

Gwamnatin Amurka za ta ci gaba da gano irin wadannan damar don kara ma al'ummar Iran karfin gwiwa wajen magana cikin 'yanci ba tare da fargabar fuskantar bita da kullen gwamnati ba.

Wannan sharhin Muryar Amurka ne mai bayyana ra’ayin Gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG