Accessibility links

Breaking News

Samar Da Zaman Lafiya A Kan Iyakar Isra’ila Da Lebanon  


Wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas Green-Field
Wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas Green-Field

Ambasada Wood ya ce: "Babu wata gardama cewa Iran, a fili take keta takunkumin makamai a cikin kudiri na 1701, tana ba Hezbollah mafi yawan makaman roka, makamai masu linzami da jirage mara matuka da ake harbawa Isra'ila."

A shekara ta 2006, bayan kazamin fada tsakanin Isra'ila da Hezbollah, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kuduri mai lamba 1701. A cikin shekaru 18 da suka wuce, an samu zaman lafiya akan iyakar da ta raba kasar Lebanon da Isra'ila da Tuddan Golan.

"Amma duk da haka, wannan zaman lafiyar ya wargaje ne a safiyar ranar 8 ga watan Oktoba lokacin da kungiyar Hezbollah ta kaddamar da hare-haren rokoki a kan Isra'ila, kuma 'yan ta'adda dauke da makamai suka kutsa kai cikin Isra'ila daga layin Blue Line bayan harin ta'addanci da Hamas ta kai wa Isra'ila," in ji Mataimakin Wakilin Amurka na Musamman na Siyasa a Majalisar Dinkin Duniya.

“Hezbollah ta yanke shawarar kai harin bama-bamai a arewacin Isra’ila. Kuma a cikin watanni 11 da suka gabata ta ci gaba da yin haka a kusan kullum.”

Ambasada Wood ya ce "Ba daidai ba ne cewa har yanzu majalisar ba ta yi Allah-wadai da kungiyar Hezbollah ba game da wadannan matakai na ta da zaune tsaye."

"Munanan hare-haren ta'addanci na Hezbollah sun jefa fararen hulan Isra'ila da na Lebanon cikin hadari. Suna kawo cikas ga kwanciyar hankali da mulkin kasar Lebanon. Bai kamata Lebanon ta zama mafakar kungiyoyin 'yan ta'adda ba ko kuma wata matattarar kaddamar da hare-hare kan Isra'ila ba."

Ambasada Wood ya ce: "Babu wata gardama cewa Iran, a fili take keta takunkumin makamai a cikin kudiri na 1701, tana ba Hezbollah mafi yawan makaman roka, makamai masu linzami da jirage mara matuka da ake harbawa Isra'ila."

“Bari mu fayyace, Isra’ila na da ‘yancin kare kanta daga hare-haren Hezbollah. Babu wani ‘dan wannan Majalisar da ke fuskantar mummunar kungiyar ta'addanci a kan iyakarsa, da zai amince da kai hare-hare a kullum da kuma raba dubun-dubatar al'ummarta. Amurka tana goyon bayan 'yancin Isra'ila na kare kanta, kuma za mu ci gaba da yin aiki don tabbatar da zaman lafiya a yankin."

Ambasada Wood ya jaddada cewa: "Ba ma son ganin rigingimu sun tsananta da kuma yaduwa." Musamman, Rundunar Majalisar Dinkin Duniya a Labanon, ko UNIFIL, tana taimakawa wajen inganta kwanciyar hankali ne a kan iyakar Isra'ila da Lebanon.

Domin tunkarar gaba, in ji Ambasada Wood, wannan Majalisar na bukatar ganin an aiwatar da kudurin 1701, wanda ya hada da kafa wani yanki a kudancin Kogin Litani wanda ba shi da wani jami'i da ke dauke da makamai, kadarori ko makaman da ba na gwamnatin Lebanon da UNIFIL ba. Yana da matukar muhimmanci UNIFIL ta sami damar saka idanu da kuma ba da rahoton duk wani aiki da ya saba wa ƙudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na 1701.

Tsawaita wa'adin UNIFIL zai tabbatar da muhimmin ginshiƙi na kwanciyar hankali a Lebanon ya kasance a wurin don taimakawa wajen wanzuwar zaman lafiya.

Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG