A yau, kusan mutane biliyan biyu ke rayuwa a yankunan da rikici ya shafa. Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta ce, "Nauyinmu ne”, mu hana wani mutum ko da guda daga fuskantar ukubar da ke tattara da yaki."
Labari mai dadi, in ji Ambasada Thomas-Greenfield, shi ne "mun san yadda ake samar da yanayin da zai samar da zaman lafiya." Mataki na farko shi ne matsawa daga kalmomi mu koma saka hannu wajen hana faruwa.
“Rigakafin na bukatar dogon lokaci, dalla-dalla, da hanyoyin da suka haɗa da; buƙatar manufofinta siyasa, haɗin gwiwa mai inganci, albarkatu masu dorewa, da mallakar ƙasa. An nuna ci gaban dabarun rigakafin kasa don taimakawa wajen magance matsalolin rikice-rikice da karfafa abubuwan more rayuwa na kasa don samar da zaman lafiya.”
Tare da cikakken bayani da goyon baya, dabarun rigakafin za su iya ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, inganta tsarin doka, ƙarfafa ƙungiyoyin jama'a, da haɓaka juriya da haɗin kai na zamantakewa.
Ambasada Thomas-Greenfield ta ce "zaman lafiya, ci gaba, da ayyukan jin kai sun dogara da juna da karfafa gwiwa." Ta kuma bukaci kasashe mambobin kungiyar su ci gaba da koyo daga juna game da rigakafin rikice-rikice. Ambasada Thomas-Greenfield ta ce kasar Saliyo ita ce misali.
“Saliyo ta samu ci gaba sosai wajen sake ginawa da ƙarfafa cibiyoyin da yaƙi ya shafa bayan yaƙi da kuma magance wasu bukatu na gaggawa na mutanenta da waɗanda yaƙi ya shafa, haɗe da kafa wata hukuma Truth and Reconciliation Commission.
Asusun gina zaman lafiya ga Saliyo The Peacebuilding Fund ya haɗa da mayar da hankali sosai kan rikice-rikicen ƙasa, raunin iyakoki da kan iyakoki, da ƙarfafa mata da matasa da kuma shiga tsakani."
Don yin tasiri, tilas ne matakan rigakafin rikice-rikice da samar da zaman lafiya su kasance tare, in ji Ambasada Thomas-Greenfield:
“Lokacin da mata, matasa, da wasu wadanda ma ba a cika jin muryoyin su ba idan za su shiga a dama da su, daidai, da kuma ma’ana a harkokin siyasa da na jama’a, tsare-tsare da aiwatarwa za su iya nuna bukatun dukkan jama’a, kuma akwai yiwuwar yin hakan, na sakamako mai ɗorewa kuma mai dorewa ga kowa.”
Taron koli na gaba na wata mai zuwa da kuma na gaba na 2025 Future and the subsequent 2025 Peacebuilding Architecture Review akan gine-ginen zaman Lafiya hanyoyi ne masu muhimmanci don ƙarfafa ƙoƙarin gina zaman lafiya, ciki har da rigakafin rikici da shiga tsakani.
Amurka na ci gaba da jajircewa kan yunkurin Majalisar Dinkin Duniya na rigakafin rikice-rikice da samar da zaman lafiya ta hanyar shirye-shiryenta na shekaru 10 a kasashe hudu da suka fi fifiko, wato Haiti, Libya, Mozambique, da Papua New Guinea, da kuma yankin gabar tekun yammacin Afirka.
Amurka za ta ci gaba da goyon bayan shirye-shiryen Majalisar Ɗinkin Duniya, na ci gaba da yin rigakafin rikice-rikice, da sasantawa, da yunƙurin zaman lafiya. Sannan ta bukaci kowace kasa mamba ta yi hakan.
Wannan sharhin ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.