Accessibility links

Breaking News

Akwai Bukatar Gaggauta Aiki Tare Don Yaki Da Manyan Laifuka Na Matakin Kasa Da Kasa


Kotun Manyan Laifuka Na Kasa da Kasa ICC
Kotun Manyan Laifuka Na Kasa da Kasa ICC

Yadda kimiyyar na’urorin kwamfuta da kayan aikin lataroni ke dada bunkasa da sauri, alama ce dake nuna cewa kimiyyar za ta inganta rayuwarmu sannan za ta sauya yadda ake gudanar da al’amuran kamfanoni. Sai dai kuma, ana samun koma baya a bangaren dabarun shawo kan matsaloli a kamfanoni da bangaren ala’muran shari’a, lamarin da ya kasance babban hadari ga rayuwar al’ummar duniya.

Jakadan Amurka kan al’amuran tattalin arziki da al’amuran al’umma a Majalisar Dinkin Duniya, Ed Heartney ya ce wajibi ne mu yi aiki domin tabbatar da nagarta a sa’ilin da ake tsarawa, kerawa, da kuma yadda ake amfani da wadannan fasahohi. “ Bai dace a ce ana ko in kula da al’amuran hakkin bil-Adama ba, sannan ya kamata batun hakkin dan Adam ya kasance kan gaba a duk wata yarjejeniyyar kasa da kasa da zai tabbatar da tsari mai nagarta da zai jagoranci yadda ake gudanar da al’amura a fannin fasahar lataroni.

Yadda ake samun hauhawar masu amfani da fasahar ta hanyoyin da basu dace ba wajen bincike (sa ido) zaluntar kasashe, leken asiri ba tare da izini ba da kuma sauran laifuka da suke da alaka da take hakkoki da yada labaran kanzon kurege ya zama abun damuwa ga Amurka. Amfani da wadannan fasahohi ta wadannan haramtattun hanyoyi ya dada ta’azara a wasu kasashe inda dokokin kasashen suke dakile kokarin masu yunkurin kalubalantar gwamantocinsu cikin lumana sannan a wani bangeren kuma su takaita ayyukan ‘yan jarida na kwarai”.

Heartney ya ce, “ mun damu matuka da yadda ake samun karuwar amfani da manhajojin leken asiri na kasuwa wajen kai hari wa masu kare hakkin bil-Adama, ‘yan raji, ‘yan jarida da duk wani da ake ganin zai kalbalanci wani lamari, kazalika jakadu da iyalensu ma ba su tsira ba.

“Ana yi wa masu fafutukar kare hakkokin mata barazana. Ana kai hari wa ‘yan jarida masu bada rahotanni masu sahihanci kan rasahawa da mulkin kama karya. Misali, kwararu akan kungiyoyin al’umma sun ruwaito cewa an dasa na’urar liken asiri a wayar wani gogagen dan jaridan kasar Rasha. Ire-iren wannan batutuwan zalunci a fannin lataroni din zai iya kaiwa ga zalunci a zahiri da suka hada da tsare mutum ba bisa ka’ida ba, garkuwa, har ma ya kai ga kisar gilla a wasu lokutan idan ba a yi sa’a ba.

“Freedom Online Coalition, wata kungiyar kasashe da suke mai da hankali wajen bada goyon baya ga mutumta hakkokin mutane yayin amfani da kafen yanar gizo da kuma al’amuran digital, a ‘yan kwanankin bayan nan, sun mai da hankali akan wasu daga cikin wadannan kalubalolin,” a cewar Kansila Heartney.

Amurka na nan kan bakarta ta aiki tare da masu ruwa da tsaki kan dabarun inganta harkokin kirkira da kuma bunkasa kudaden shiga a bangare guda yayin da a daya bangaren kuma, a mutumta hakkokin dan Adam a fadin duniya.

“Muna kira ga gwamnatocin kasashe su hada hannu da mu domin daukan matakai masu ma’ana da zummar dakatar da amfani da manhajoji ta hanyar da basu dace ba, sannan mu inganta amfani da su kamar yadda ya kamata da zai dace da dokokin hakkin bil-Adama a fadin duniya, kana wanda zai haifar da damar kasuwanci mai ma’ana.

Anncr: Sharhin Muryar Amurka kenan mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka

XS
SM
MD
LG