Accessibility links

Breaking News

Rikici Shi Ne Silar Jefa Bil Adama Cikin Mawuyacin Hali


Samantha Power
Samantha Power

"Dole ne mu yi amfani tsarin diflomasiyya na duniya don kawo karshen wadannan rikice-rikice," a cewar Power.

Shugabar Hukumar USAID Samantha Power ta ce "Ana fargabar sama da kwatan biliyan na mutane za su kasance masu neman a tallafa musu a shekarar 2022, wanda ya dara abin da aka kwashe tsawon shekara goma ana gani a wannan shekara.

“Wannan annoba mai naci, wacce ke ci gaba da daukar rayuka, barnata tattalin arziki tare da jefa mutane cikin halin kakani-kayi. Fiye da kashi ɗaya cikin ɗari na mutanen duniya sun kaura. Rashin abinci da ba a taɓa yin irinsa ba. Rikice-rikice akai-akai da suka ki karewa, da sauyin yanayi da ke kunno kai a kan su duka, yana kara ta'azzara hasara da rashin samun nasara."

Da take magana a wani taron jin kai na Majalisar Dinkin Duniya na 2022 ta yanar gizo, Power ta lura cewa "babban tushen bukatun jin kai a duniya a yau ba daga annoba ko bala'o'i na halitta ba ne - daga rikici-rikice ne," akwai bukatan canjin da zai wuce buƙatar ƙarin albarkatu.

"A dauki misalin Yemen, Syria, Somalia, Sudan ta Kudu, wadannan rikice-rikicen da aka dade ana yi a wadannan kasashen ya zame masu fitina ga al’umarsu kuma suna barazana ga zaman lafiya da ya zarce har ga iyakokinsu. A wannan shekarar da ta gabata mun ga juyin mulkin da aka yi a Burma, da faduwar Afganistan a hannun 'yan Taliban, da mamayar da sojoji suka yi a Sudan, da kuma matsalolin da mutane suka shiga a Habasha.

Da yawa daga cikin wadannan al’amura, gwamnatocin wadannan jahohi masu rauni ko wanda rikice-rikice ya addabe su, sun kasa biyan bukatun al’umarsu, sun fi zabar tashin hankali kan su mika ko raba mulki ko mutunta hakki.”

Wannan na nufin cewa "Yayin da waɗannan rikice-rikicen ke ci gaba, hakkin matsalar da ke biyo bayanta na rashin adalci a halin yanzu yana kan ƙungiyoyin jin kai," a cewar Power.

Amsar ta siyasa ce, in ji ta. "Kuma shi ne dalilin da ya sa yana da mahimmanci cewa Amurka da sauran ƙasashe su yi abin da Shugaba Biden ya kira diflomasiyya mai ɗorewa."

"A duk lokacin da rikici ya taso ko matsalar yanayi ta jefa mutane cikin hatsari, Amurka za ta taimaka kuma za ta ba da tallafi. Amma a cikin duniyar yanzu da ta canza tare da buƙatu masu girma da ke ci gaba da karuwa, ba za mu iya ci gaba da yin abu daya ba, da kuma ba da manya-manyan tallafi, sannan kuma mu sa ran sakamakon zai banbanta.”

"Dole ne mu yi amfani tsarin diflomasiyya na duniya don kawo karshen wadannan rikice-rikice," a cewar Power. "Muna buƙatar nemo hanyar da za mu yi amfani na tattauna shawarwarin diflomasiyya a shiyya-shiyya, a matsayin mu na Majalisar Ɗinkin Duniya, da kuma dangantakar da ke tsakaninmu da kuma haɗuwa a matsayin ƙawayen juna, don ƙoƙarin haɗa ɓangarorin domin a kawo ƙarshen rikice-rikicen"

XS
SM
MD
LG