"A yau Bosnia da Herzegovina sun sami kansu a wata mararraba ana kuma samun shakku kan dorewar zaman lafiya na tsawon shekaru 26,” yayin da shugabannin kasar ke kokarin shuka rarrabuwar kawuna, in ji shugabar hukumar raya kasashe ta Amurka Samantha Power a ziyarar da ta kai a baya-bayan nan.
Power ta gana da dukkanin mambobin gwamnatin Bosnia da na Herzegovina guda uku, ciki har da shugaban Sabiyawan Bosnia mai neman ballewa, Milorad Dodik, wanda ya yi barazanar janye Sabiyawan daga rundunar sojan kasa, shari'a, da tsarin haraji a wannan shekara. Ta kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya da kuma hadarin da ke tattare da kamalami masu haddasa rarrabuwar kawuna da wasu ayyuka makamantan hakan.
Mai Gudanarwar Power ta jaddada "bukatar hadin kai da kwanciyar hankali don samun ci gaban tattalin arziki da wasu hanyoyi." Magana game da yaki yana kawo wahala wajen jawo masu saka hannun jari mai inganci ko gina kakkarfan tattalin arziƙin da ya dace don matasa da sauran mutane.
"Samun makoma mai kyau abu ne mai yiwuwa," in ji ta. Amma yana buƙatar dukkan 'yan siyasa su yi watsi da ayyukan da ke haddasa rarrabuwar kawuna da maganganu masu tayar da hankali, a dakatar da hare-haren da ake kaiwa cibiyoyin Bosnia da Herzegovina. Kuma a ba da himma wajen kawo sauye-sauyen dimokradiyya da aka dade ake bukata."
“’Yan ƙasar nan ba sa son komawa ga abin da ya faru a baya,” in ji Power, “amma kuma ba sa son a ci gaba da halin da ake ciki, haka ita ma Amurka. Kuna son ku samu makomar dimokuradiyya da ya cancanta ba tare da cin hanci da rashawa ba kuma wadda babu rikici na kabilanci."
Kusan kashi 75 cikin 100 na mutanen Bosnia da Herzegovina sun goyi bayan dadadden burinsu na shiga Tarayyar Turai, amma wannan ba abu ne mai sauƙi ba, bugu da kari ga kalubalen siyasa na baya-bayan nan, Bosnia da Herzegovina na fuskantar kalubalen tattalin arziki. Kasar na asarar masu zuba jari masu zaman kansu, inda a yanzu bangaren ‘yan kasa ke wakiltar kusan kashi 70 na tattalin arzikin kasar. Kuma matasa na fuskantar matsalar rashin aikin yi mafi yawa a nahiyar.
Amurka ta ba da taimakon dala biliyan 2 ga Bosnia da Herzegovina tun daga 1996. Amurka za ta ci gaba da tallafawa kokarin yaki da cin hanci da rashawa mai, 'yancin kafofin watsa labarai, da sauye-sauyen tattalin arzikin Bosnia da Herzegovina.
Makoma mai inganci karkashin tsarin dimokraɗiyya ga Bosnia da Herzegovina, ita ce wacce za a iya cim ma, idan ’yan siyasar ƙasar suka saurari jama’arsu, suka rungumi zaman lafiya da kawo sauyi, da yaƙi da cin hanci da rashawa da ke hana ci gaba da kuma sa matasa yin hijira.