A ziyararsa ta baya-bayan nan a Afirka, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya bayyana wasu fanni biyar da Afirka da Amurka suke da sha’awar yin hulda a tsakaninsu.
Fanni na farko shi ne yadda za a gina tattalin arzikin duniya na bai-daya.
Shirin bunkasa tattalin arziki na “Prosper Africa” shiri ne da ke da muradin yaukaka harkokin kasuwanci da duka bangarorin biyu za su amfana.
Dokar ci gaban Afirka da dama ta ba da damar shiga kasuwannin Amurka ba tare da haraji ba, kuma Amurka na kokarin ganin kasashen Afirka sun ci moriyarsa. Har ila yau, Amuka na maraba da yankin ciniki cikin 'yanci na Nahiyar Afrika, a matsayin hanyar da za ta bunkasa ciniki tsakanin Afrika.
Fannin a biyu kuma shi ne, yadda za a hada kai a magance matsalar sauyin yanayi, in ji Sakatare Blinken:
“Irin mummunan tasirin da sauyin yanayi ke yi, abu ne da ake gani a bayyane a sassan nahiyar – yunwa, sare dazuzzuka, rashin amfanin gona, ambaliya, kwararar hamada, rashin abinci, gasa don neman albarkatu, rugujewar tattalin arziki da ƙaura."
Tafkin Chadi ya kasance muhimmin waje na samun albarkatunruwa, abinci, abubuwan rayuwa ga mutane shekaru aru-aru. Yanzu ya kusan kafewa - ya ragu zuwa kashi ɗaya bisa ashirin kamar yadda yake da shekaru 60 da suka wuce. "
Shirin gaggawa na Shugaba Joe Biden na daidaitawa da juriya zai tallafa wa shirin daidaita al'amuran Afirka da shugabannin kasashe a fadin Afirka suka kaddamar, wanda ke da nufin tsarawa da kuma samar da kayan more rayuwa masu amfani da makamashi da juriya ga sauyin yanayi.
Fannin a uku a cewar Sakatare Blinken, "dole ne mu kawo karshen annobar ta COVID-19." A baya-bayan nan Amurka ta cimma kai alluran rigakafi miliyan 270 a duk fadin duniya. Fiye da miliyan 70 na wadannan alluran an aika zuwa kasashe 43 na kudu da hamadar Sahara, kuma wasu na kan hanya.
Fanni na hudu shi ne, karfafa dimokradiyya a Afirka. Koma baya da tsarin dimokradiyya ke fuskanta a duk duniya na ci gaba da zama abin damuwa. Bugu da kari, ana amfani da fasahar zamani don kai hari ga 'yan kasa da kuma rufe bakinsu. Sakatare Blinken ya ce "Dole ne dimokuradiyya ta amsa kiran yaki da gurbatattun bayanai, tsayawa tsayin daka kan 'yancin Intanet, rage amfani da fasahar sa ido ta hanyar da ba ta dace ba, da kafa ka'idojin da suka dace a sararin samaniya," in ji Sakatare Blinken.
A karshe, dole ne a samar da dawwamammen tsaro da zaman lafiya a Afirka. Barazana da masu tsattsauran ra'ayi, da masu aikata laifuka, da rikice-rikicen cikin gida ke yi na gaske ne, in ji Sakatare Blinken. Wani bangare na amsar, shi ne kwararrun jami'an tsaron kasa da jami'an tsaro na gida wadanda za su iya kare 'yan kasa tare da mutunta 'yancin dan adam. Amma magance tushen rikice-rikice yana da mahimmanci.
Sakatare Blinken ya ce, "Amurka na son karfafa hadin gwiwarmu a fadin Afirka ta hanyoyin da za su biya bukatunku, da muradunmu, da kuma muradun mutanen duniya wadanda rayuwarsu da makomarsu ta dogara ne kan abin da za mu iya cimma tare."