Accessibility links

Breaking News

TAYIN TUKWICIN NEMAN KAMA SHUGABANNIN MASU AIKATA LAIFIN YANAR GIZO NA SODINOKIBI


Amurka ta kuduri aniyar ladabtar da duk wadanda ke kai harin yanar gizo kan muradun Amurka da na kawayenta.

Don ta karfafa kudurinta na magance [manyan laifukan yanar gizo], Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar za ta ba da tukwicin har zuwa $10,000,000 ga duk wanda ya ba da bayanin da zai kai ga ganowa ko wurin buyar duk wanda ke riƙe da wani matsayi na jagoranci a cikin ƙungiyar aikaata manyan laifukan yanar gizo a matakin kasa da kasa mai suna Sodinokibi. Bugu da kari, Ma’aikatar za ta ba da tukwicin da ya kai har zuwa $5,000,000 ga duk wanda ya bayar da bayanin da ya kai ga kamawa ko gurfanar da mai laifun a kowace kasa muddun ya taka rawa ko ya hada baki ko kuma y ana niyyar hada baki a aika aikar yanar gizo ta sodinokibi.

Kungiyar masu aikata laifukan yanar gizo ta Sodinokibi , wacce aka fi sani da REvil, ita ce ke da alhakin aukuwar laifukan yanar gizo wanda ya shafi JBS Foods, mai samar da kayayyakin amfanin gona da farko zuwa kasashen Australia da Amurka, wanda ya haifar da cikas wajen sarrafa abinci da isar da abinci. Sodinokibi kuma ya lalata Kaseya, kamfanin fasaha wanda ke ba da sabis na hanyar sadarwa, aikace-aikace, da ayyukan ababen more rayuwa ga dubban ƙananan kamfanoni da masu samar da sabis. Lamarin ba wai kawai ya shafi ayyukan Kaseya ba, har ma da na abokan cinikinsa a duniya.

Ana bayar da wannan tukwicin a ƙarƙashin Shirin Ba da Ladan Don Dakile Laifukan Kasa da Kas ana Ma’aikatar Harkokin Wajen. Ma’aikatar ta na kula da shirin tare da haɗin gwiwar abokan aikinta wadanda aikinsu ne tabbatar da bin doka na tarayya don taka burki da kuma wargaza ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka a duniya, gami da laifukan yanar gizo.

Masu aikata laifuka sama da 75 da manyan masu safarar muggan kwayoyi ne aka gurfanar da su gaban kuliya a karkashin shirin bayar da lada don dakile laifuffuka na kasa da kasa da kuma shirin bayar da lada don dakile miyagun kwayoyi tun daga shekarar 1986. Ma’aikatar ta biya fiye da dala miliyan 135 a matsayin tukwicin.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Ned Price ya ce, "Amurka ta ci gaba da dagewa wajen kare duk wadanda abin ya shafa a fadin duniya daga cin zarafin masu aikata laifuka ta yanar gizo," Ya kara da cewa "kuma muna sa ido ga kasashen da ke bayar da mafaka ga masu aikata laifukan yanar gizo da su tabbatar da adalci ga 'yan kasuwa da kungiyoyin da lamarin ya shafa. .”

XS
SM
MD
LG