Amurka Ta Sanya Takunkumi Ga Dukkan Masu Tallafawa Hezbollah a Lebanon

Antony Blinken

A ranar 18 ga watan Janairu ne Amurka ta kakaba takunkumi kan wasu jami'an kungiyar Hizbullah guda uku da ke da alaka da harkokin kudi da kuma kamfaninsu na balaguro da ke Lebanon. Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana a cikin wata rubutacciyar sanarwa cewa: "Muna daukar wannan matakin ne domin nuna goyon baya ga al'ummar kasar Lebanon, wadanda har yanzu ayyukan cin hanci da rashawa na Hizbullah na barazana ga tsaro da 'yancinsu."

Mutanen uku sun hada da Adel Diab, Ali Mohamad Daoun, da Jihad Salem Alame; kasuwancin da suka kafa shine Dar Al Salam na Balaguro da yawon bude ido. An sanya sunayen ne a karkashin dokar zartarwa mai lamba 13224, wacce ke bin sawun 'yan ta'adda, shugabanni, da jami'an kungiyoyin ta'addanci, da masu bayar da tallafi ga 'yan ta'adda ko ayyukan ta'addanci.

A ranar 21 ga watan Janairu, Amurka ta kuma ayyana wani jami'in harkokin kudi na kungiyar Hizbullah Adnan Ayad, da kuma mambobin cibiyar sadarwa na kasa da kasa na gudanarwa da kamfanoni da ke da alaka da shi da Adel Diab, abokin kasuwancin Ayad kuma dan kasuwan Hizbullah, a karkashin wannan hukuma.

Amurka ta ayyana kungiyar Hizbullah a matsayin kungiyar ta'addanci ta kasashen waje a ranar 8 ga Oktoba, 1997, sannan a matsayin kungiyar ta'addanci ta musamman ta duniya a ranar 31 ga watan Oktoban 2001.

Hizbullah dai ta dauki alhakin kai wasu munanan hare-haren ta'addanci a duniya, ciki har da harin bam na barikin ruwan Amurka da ke Beirut a shekarar 1983, wacce ta kashe jami'an Amurka 241, cibiyar al'ummar Yahudawa ta AMIA a shekarar 1994 da ke Buenos Aires wacce ta kashe 85 tare da raunata ɗaruruwa, da kuma kisan tsohon Firaministan Lebanon Rafic Hariri a 2005, wanda shima aka kashe wasu 22 tare da raunata 226.

A cikin wata sanarwa a ranar 18 ga watan Janairu, Ma'aikatar Baitulmalin Amurka ta ce, “wannan ayyana sun da baitul malin Amurka ke yi, wani yunkuri ne na ci gaba da dakile ayyukan kungiyar ta Hezbolla wacce ke ci gaba da kaucewa takunkumin da ake saka mata a duniya.”

Kasar Lebanon wadda a da ke samun ci gaba, a halin yanzu na cikin wani mawuyacin hali na tattalin arziki, inda kashi uku cikin hudu na al'ummar kasar ke fama da talauci.

Karkashin karamin sakataren baitul malin yaki da ayyukan ta'addanci da leken asiri Brian Nelson ya rubuta cewa, "Hizbullah na da'awar cewa tana goyon bayan al'ummar Lebanon, amma kamar sauran masu cin hanci da rashawa a Lebanon da baitul mali ta ayyana, Hizbullah na ci gaba da samun riba daga sana'o'in kasuwanci da aka kebe da kuma yarjejeniyoyin siyasa da ake yin su a boye, tare da tarin dukiyar da al'ummar Lebanon ba ta taba gani ba."

Sakataren harkokin wajen Amurka Blinken ya ce, Hizbullah da kawayenta sun fi mayar da hankali wajen ciyar da bukatun kansu da na majiyarsu ta Iran maimakon jin dadin al’umar kasar ta Lebanon.

Amurka za ta ci gaba da daukar matakai na dakile ayyukan Hizbullah mai hatsari da tada zaune tsaye.