Manyan Laifukan Yaki A Sudan

Blinken

Sakataran Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, mambobin Dakarun Sojin Sudan wato SAF da mambobin Dakarun Sa Kai na RSF sun aikata laifukan yaki a Sudan.

Sakatare Blinken ya kara da cewa Amurka ta kuma yi matsayar cewa, “mambobin dakarun RSF da kawayensu ‘yan bindiga sun aikata laifuka cin zarafin bil’adama da kuma kisan kawar da wata kabila.” Musamman ya kuma ambaci cewa, farauta da kashe fararen hula kabilar Masalit da aka bar gawarwakin su a kan tituna.”

Sakatare Blinken ya ce matsayar ta kumshi “samar da dakaru da sabunta makamashi ga ‘yan Afirka da kokarin da kasashen duniya domin kawo karshen tashin hankalin.”

Sudan ta fada cikin mummunan rikici tun a watan Afrilun 2023 lokacin da fada ya barke tsakanin dakarun sojin kasar da dakarun sa kai na RSF, wanda ya kawar da fatan samun komawa tsarin mulkin dimokaradiyya a kasar da ta yi fama da mulkin kama karya.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, an kashe fiye da mutane 12,000 a Sudan tun daga watan Afrilu, “ciki har da mutane 1,300 da aka kashe tsakanin 28 ga watan Oktoba zuwa 24 ga watan Nuwamba.”

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen AMurka Matthew Miller ya ce, “dole ne SAF daRSF su kawo karshen wannan mummunan rikici.”

”Mun tattara bayanan ayukan cin zarafin bil adama da aka yi ta maimaitawa. Mun tattara bayanan dakarun bangarorin da ke shiga kawai suna aiwatar da kisan fararen hula gaba-gadi a kauyuka. Mun ga bayanan suna shiga makarantu suna neman inda yaran maza suke, da kuma inda manyan mutane suke, don su kashe su. Mun ga bayanan da suka shafi fyade a fakaice.”

Ya bayyana cewa “da dadewa ‘yan tawayen sun kashe fararen hula, sun yi musu fyade, da kuma kai musu hari ba tare da wani hukunci ba a Sudan.”

“Dole ne kasashen duniya sun yi aiki don tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa da al’ummomin da lamarin ya shafa tare da kawo karshen wannan zalunci. Yayin da muke aiki tare da takwarorinmu na Afirka, Amurka ta yi kira ga dukkan kasashe da su goyi bayan kokarin kare fararen hula a Sudan, da hana cin zarafi a nan gaba, da kuma yin kira ga a hukunta wadanda ke da hannun a wadannan munanan ayukan.”

Miller ya yi nuni da cewa, a can baya Amurka ta kakaba wasu jerin takunkumai ga daidaikun mutane da hukumomi da ke da alhakin kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da cin zarafin bil adama a Sudan, kuma za ta yi amfani da dukkan karfin da muke da shi, don taimakawa wajen kawo karshen rikicin.

‘Amurka,” in ji shi, “tana tare da al’ummar Sudan, wadanda ba su nemi wannan yakin ba, don goyon bayan bukatunsu masu na komawa kan tafarkin dimokaradiyya da ‘yanci da zaman lafiya da adalci.”

Anncr: An saurari Sharhin Muryar Amurka mai bayyana ra'ayin gwamnatin Amurka.