Muradun Amurka Da Columbia Na Bai Daya

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken

Yanzu kuma sai sharhin Muryar Amurka wanda ke bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka

Wata gagarumar tattaunawa ta kwanan nan tsakanin Amurka da Colombia ta jaddada aniyar nan ta magance matsalolin juna.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce “an gina tattaunawar ne a kan manufofi iri daya na manyan kasashen biyu masu bin tafarkin dimokaradiyya da suka himmantu ga ci gaba da gina al’ummarsu.”

Ministan harkokin wajen Colombia Alvaro Leyva ya ce “Mu mutane daya ne, daga nahiya daya, sha’anin tsaro iri daya, batutuwa iri daya.”

A cikin batutuwa da aka tattauna a kai, Blinken ya jaddada batun sauyin yanayi da kasuwanci.

"Za mu ci gaba da aiki don taimaka wa Colombia ta cimma burinta a kan batun yanayi, kama daga samar da taimako a fannin fasahar makamashi na iska da hasken rana da ake yi yanzu, don karfafa aikin kare gandun dajin Amazon," in ji Sakatare Blinken. "Za mu fadada hanyoyi ga manoma, masu sakin zani, da sauran kanana da matsakaitan 'yan kasuwa a yankunan karkara don kai kayayyakinsu zuwa kasuwannin duniya da kuma cin gajiyar yarjejeniyar ciniki tsakanin Amurka da Colombia."

Tattaunawar ta kuma mayar da hankali kan inganta tsaron fararen hula. Za a ci gaba da aiwatar da doka, amma kasashen biyu sun amince, in ji Sakatare Blinken, yana mai cewa "dole ne mu magance tushen rashin tsaro - kamar cin hanci da rashawa, kamar rashin hukunta masu laifuka, cin zarafin bil'adama da kuma rashin samun dama a fannin tattalin arziki." Don haka ne Hukumar Raya Kasashe Masu Tasowa (USAID) ke zuba jarin dala miliyan 60 cikin shekaru biyar don fadada damarmaki ga al'ummomin Afro-Colombian da 'yan asalin kasar Colombia.

Bugu da kari, Amurka tana sane da mummunan halin da rashin tsaro ke haifarwa a yankunan karkara wajen kare lafiyar masu kare hakkin bil'adama, shugabannin kabilu, da masu kare muhalli don haka hadin gwiwarmu da ke ci gaba yanzu zai yi kokarin magancewa, ragewa, da kuma hana ci gaba da cutarwa.

Har ila yau an mayar da hankali kan dakile kwararar miyagun kwayoyi. Sakatare Blinken ya ce, "Tsarin da ya dace," shine neman rage bukatun magunguna ta hanyar gudanar da bincike kan amfani da abubuwa, rigakafi, jiyya, da murmurewa, da kuma gano hanyoyin da za a rage raba miyagun magungunan ta hanyar shiga tsakani, da samar da al'ummomin da ke da rauni wasu hanyoyin samun kudi.

Sakatare Blinken ya lura da yawan kaura da ba a taba ganin irinsa ba a duk faɗin duniya. A martaninsa ga bakin haure na Venezuela, "Colombia," ya ce, "lamarin na nuna cewa idan aka magance kaura cikin aminci, cikin mutuntaka, kuma a matsayin yanki, na iya habaka kwanciyar hankali kuma yana iya zama dama, ba nauyi ba, ga al'ummomi.”

Tun daga 2010, Amurka da Colombia sun shiga cikin Tattaunawar Manyan Matakan guda goma. Tattaunawar ta wannan shekara ta sake tabbatar da aniyar ci gaba da cimma burin da aka sa gaba a cikin hidimar samar da ingantacciyar rayuwa, dimokuradiyya, da amintacciyar makoma ga yankin.

Wannan shine sharhin Muryar Amurka da ya bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.