Nicaragua ta dauki matakin na karshe da zai haramta gudanar da sahihin zabe. A ranar 6 ga watan Agusta, babbar majalisar zaben kasar ta haramtawa bangaren ‘yan adawa tsayawa takara a zaben 7 ga watan Nuwamba.
Hukuncin bai kamata ya zama abin mamaki ba, tun da, kamar yadda rahoton kare hakkin dan adam na Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya nuna, jam’iyyar “shugaba Daniel Ortega ta Sandinista National Liberation Front, na da iko da bangaren gudanarwa da majalisar dokoki da shari’a da kuma hukumomin zabe.
Sakataren Harkokin Wajen Antony Blinken ya fada a cikin wata sanarwa cewa haramta jam’iyyar ‘yan adawa da ta rage a Nicaragua, na nuni da yadda Ortega da uwargidansa kuma mataimakiyar shugaban kasa Rosario, suka kuduri aniyyar ci gaba da zama akan karagar muli ta ko wane hali.”
Ya lura cewa soke takarar jam'iyyar adawa "ya biyo bayan tsare 'yan takarar shugaban kasa guda bakwai da ‘yan adawa 24, masu fafutukar kare hakkin dan adam, shugabannin kasuwanci, dalibai da ma'aikatan kungiyoyi masu zaman kansu a cikin watanni biyu da suka gabata."
Shugaba Ortega yana neman tabbatar da wa'adin mulkinsa na hudu kuma ya kuduri aniyar hana wani abinda zai iya kawo cikas - tabbas ba tsarin dimokradiyya ba, cibiyoyi, ko masu ba da shawara. Sakataren Blinken ya ce zaben da aka yi a Nicaragua "gami da sakamakon sa na karshe, ya rasa dukkan sahihancin sa."
A wani mataki na mayar da martani dangane da yadda tauye tsarin dimokradiyya da na hakkin bil adama, a ranar 9 ga watan Yuni Amurka ta saka takunkumi akan mambobin gwamnatin Ortega su hudu. A ranar 1o ga watan Yuli, Amurka ta saka takunkumi hana biza akan wasu ‘yan majalisar dokokin Nicaragua, alkalai da masu shigara da kara da kuma iyalansu su 100
A kuma ranar 6 ga watan Agusta, Amurka ta takaita biza na wasu dangi guda 50 na wakilan Majalisar Nicaraguan da masu gabatar da kara da alkalai na Nicaraguan. A cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price, “Duk wanda ya ci gajiyar murkushe zabe na gaskiya a Nicaragua ba a maraba da shi a Amurka.
A cikin bayaninsa, Sakataren Blinken ya lura cewa gwamnatin Ortega-Murillo ta gaza cika alkawuran da ta ɗauka a ƙasashen duniya a ƙarƙashin yarjejeniyar Dimokraɗiyya ta Amurka, da kuma haƙƙin mutanen Nicaraguan na zaɓar shugabanninsu da yardar kaina.
"Za mu ci gaba da yin aiki kafada da kafada da sauran kasashe masu tsarin dimokiradiyya don mayar da martani ta fuskar diflomasiyya da tattalin arziki ga wadannan munanan abubuwan da ke faruwa, wadanda suke kara hana mutanen Nicaragua cimma burinsu na samun gwamnati ta gari da wadatar tattalin arziki."