Mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da yawan jama'a, da 'yan gudun hijira da kuma bakin haure, Julieta Valls Noyes, ta yi bulaguro kwanan nan zuwa kasashen Habasha da Chadi inda ta gana da manyan jami'an gwamnati, da shugabannin kungiyoyin agaji, da 'yan gudun hijira, domin tattauna matsalolin jinkai da na kaura a yankin tsakiya da gabashin Afrika.
A yayin ganawarta da Firaministan kasar Chadi, Succes Masra, Mataimakiyar sakatariya ta yi sanarwar samar da taimakon jinkai na sama da dala miliyan 47 ga Sudan da kasashe makwabta:
“Wannan adadin ya sa jimlar taimakon jinkai da Amurka ke bai wa mutane a Sudan da makwaftan kasashe ya kai sama da dala miliyan 968 tun daga shekarar da ta gabata. Amurka ce ke kan gaba wajen bayar da agajin jinkai ga aikin kaai daukin gaggawa na Sudan. Yanzu, mun kuduri aniyar yin aiki tare da sauran al’ummomin duniya don taimakawa wajen rage wahalhalun da ‘yan gudun hijira sama da miliyan 1 da aka tilasta musu kauracewa gidajensu sakamakon tashin hankali, yayin da da dama ke karuwa a kullum, kamar yadda na gani a ziyarar da na kai.”
Duka kasashen na Habasha da Chadi suna taka muhimmiyar rawa a hobbasar da ake yi game da Sudan da kuma ayyukan jinkai dungurungum, in ji Mataimakiyar sakatariya Noyes:
"Tun a farkon shekarar 2023, Habasha ta karbi 'yan gudun hijira kusan 50,000 daga Sudan. A daidai lokacin da ake fama da rashin kwanciyar hankali a yankin kuryar Afirka, tallafin da Habasha ke ba wa mutanen da suka rasa matsugunai yana da matukar muhimmanci. ...Gwamnatin Habasha ta yi aiki kafada da kafada da masu gudanar da ayyukan jinkai don kafa sabbin wuraren 'yan gudun hijira tare da ba da muhimmin taimako, na ceton rai ga dubun dubatan sabbin 'yan gudun hijirar."
Mataimakiyar Sakatariya Noyes ta bayyana matukar jin dadin Amurka game da karamcin da jama'ar Chadi da gwamnatin kasar suka nuna a tsawon tarihinsu a matsayin kasar 'yan gudun hijira.
"Kwanan nan, Chadi ta rungumi babban kalubale na karbar 'yan gudun hijira sama da rabin miliyan - da kuma sama da 100,000 da suka dawo - a cikin kasa da shekara guda. Mu na ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa marasa galihu a Chadi, musamman sama da ‘yan gudun hijira miliyan 1.1 da masu neman mafaka. Shirye-shiryen Amurka na tallafawa ... za su tallafa wajen kariya, matsuguni, ruwa da tsaftar muhalli, ilimi, da sauransu, ga 'yan gudun hijira, al'ummomin da ke karbar baki, da sauran wadanda rikicin Sudan ya shafa."
Hana yunwa da bala'i na dogon lokaci a Sudan na bukatar tsagaita bude wuta da kuma kai agajin jinkai ba tare da cikas ba, in ji Mataimakiyar Sakatariya Noyes. "Mu a Amurka mun kuduri aniyar yin aiki tare da gwamnatocin Habasha da Chadi, da kuma abokan huldar kasa da kasa da na cikin gida, don ba da tallafin ceton rai ga miliyoyin mutanen da rikicin Sudan ya shafa."