Da Hamas ta kai wani mummunan hari a kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, ta takalo yaki. Kuma kamar yadda aka saba gani, abin na karewa ne kan fararen hula na bangarorin biyu. Dubban mutane daga kasashe fiye da 30 ne aka kashe tare da jikkatawa a hare-haren farko na Hamas, da kuma sakamakon harin ramuwar gayya na Isira'ila.
Kafin ta fara kai hare haren bama baman, Isra'ila ta gargadi fararen hula na Gaza da su fice. Sai dai Hamas ta umurci mutane da su kasance a gidajensu, tare da toshe hanyoyi don hana su fita. A bayyane yake cewa, farar hula za su zama tamkar garkuwa ga mayakan.
"Mun san Hamas ba ta wakiltar al'ummar Palasdinu, kuma fararen hula Falasdinawa ba su da alhakin kisan kiyashin da Hamas ta yi," in ji sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken. Ya kara da cewa, "Dole ne a kare fararen hula Falasdinu."
Zirin Gaza mai tsawon kilomita 41 da fadin kilomita 6 zuwa 12 a gabar tekun Bahar Rum, yana da fadin fadin kilomita murabba'i 365. Gida ne ga mutane sama da 2,375,000. Kimanin Falasdinawa miliyan guda ne suka rasa matsugunansu a can ba tare da wata hanyar barin Gaza ba, kuma hakan na nufin taimakon jinkai na da matukar muhimmanci ga rayuwarsu.
Sakatare Blinken ya ce "Muna ci gaba da hada kai da Masar, Isra'ila, da abokan hadin gwiwa a duk fadin yankin da kuma Majalisar Dinkin Duniya don samar da hanyoyin da za su ba da damar ci gaba da kai agajin jinkai ga fararen hula a Gaza, ba tare da amfanar Hamas ko wata kungiyar ta'addanci ba."
“Amurka ta ba da karin dala miliyan 100 a matsayin taimakon jinkai ga Falasdinawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan, wanda ya kawo jimillar taimakon da muka ba wa al’ummar Palasdinawa cikin shekaru biyu da rabi zuwa sama da dala biliyan 1.6. Hakan ya sa Amurka ta kasance kasa daya tilo da ta fi kowace kasa ba da taimako ga al'ummar Falasdinu. Muna kira ga dukkan kasashe, musamman wadanda ke da mafi girman karfin bayarwa, da su shiga sahunmu wajen yin abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a yi kan halin da ake ciki a Gaza."
Sakatare Blinken ya ce "Tushen imaninmu na cewa babu wata ran farar hula da ta fi wata, shi ne ya sa mu ka tashi haikan wajen ceto rayukan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba a wannan tashin hankalin , kai da ma duk wani tashin hankali,” a cewar a cewar Sakatare Blinken. Ya kara da cewa, “Babu batun fifiko idan ana batun kare rayukan fararen hula. Farar hula farar hula ne, ba tare da la’akari da kasarsa, kabilarsa, shekaru, jinsi, ko addininsa ba.”
Anncr: Sharhin Muryar Amurka kenan mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.