Ya zama Wajibi A Daina Sace Yara A Yankunan Da Ake Tashe Tashen Hankula Ana Fitar Da Su Daga Kasashensu

UKRAINE-CRISIS/CHILDREN-RETURN

Yanzu kuma ga sharhin jaridun Muryar Amurka mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.

Sace yara ana fitar da su daga kasashensu da karfin tsiya a yankunan da ake rikici matsala ce da ake fama da ita a fadin duniya. Wadannan munanan salon cin zarafin suna aukuwa a dukkannin sassan duniya baki daya, ciki har da Najeriya, Yemen, Colombia da Ukraine.

Ambasada Robert Wood, wakilin Amurka akan al’amuran siyasa na musamman, ya yi jawabi a wani taron kolin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a kwanan baya-bayan nan.

“Sakamakon wadannan ayyuka na matukar illa kuma yana tasiri na lokaci mai tsawo,” Ya kara da cewa. “Yana hana yaran samun kuruciya mai kyau, da ilimi, da lafiya da kuma balagar zamantakewa.”

Ya kamata a dau matakai, a cewar jakada Wood, wanda ya bayyana cewa yin hakan zai taimaka wajen tabbatar da sako su lafiya kana a dawo da yaran da aka dauke, ciki har da hanyoyin shari’ar da zasu bada fifiko akan bai wa yaran kariya da kuma hanyoyin bin diddigin wadanda suke daukewa ko kuma suke tursasawa wajen kwashe yara.

Jakada Wood ya yi nuni da cewa, wadannan laifukan take hakkin bil adaman da ake aikatawa akan yaran da bangaren gwamnati da wanda ba na gwamnati ba duk suna aikatawa. “Ya kamata mu gane rawar da wadanda suke da alaka da gwamnatoci masu aikata wannan laifi suke takawa kana mu dau matakan ladabtarwa akansu” a cewarsa.

Kwashe yara ‘yan Ukraine da Rasha ta yi a lokacin da take tsakiyar mamayarta a Ukraine misali ne na cin zarafi irin na gwamnati.

“Dakarun Rasha sun kwashe dubun dubatan yaran Ukraine ta hanyar da bata dace ba daga yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye,” a cewar Ambassada Wood.

Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna yunkurin gwamnatin Rasha na yanke sadarwa tsakanin yaran da danginsu a Ukraine kuma suna sauya musu tarbiyya. Da wannan, tarayyar Rasha taka yunkurin haramta wa Ukraine damar amfana da yaran nan gaba.”

bassada Wood ya yi nuni da cewa, Rasha ta ki ta bayyana wa dangin yaran takamaiman inda yaran suke da sannan ta kuma ki yin bayanai ga gwamnatin Ukraine a game da yaran.

Wadannan irin cin zarafin da aka aikata wa yaran Ukraine, sun kasance sakamakon matakan da gwamnatin Rasha ta dauka a dukkannin matakan gwamnati. Ya kara bayyana cewa, “Ya kamata a sanar da gwamnatin Ukraine inda aka kai yaran domin tabbatar da yunkurin maida su ga iyalansu.”

Ambassada Wood ya ce, yana da “matukar mahimmanci a dau kwararan matakai domin shawo kan mummunan take hakkin bil-adama da ake yi wa yaran da ake tursasawa sauya musu muhallai a fadin duniya, ciki har da bai wa al’ummomin da aka kwashe wa yara tallafi, tabbatar da an bai wa yaran damar neman ilimi da kuma karfafa hanyoyin hukunta masu aikata wadannan laifuka.

“Wajibi ne mu yi aiki cikin gaggawa kana mu hada karfi da karfe wajen kawo karshen kwashe yara da karfin tsiya tare da sauya musu muhalli a lokutan tashe-tashen hankula,” a cewar Ambassada Wpod. Ya kara da cewa, “wannan hakkin yaran nan ne da ya rataya a wuyar mu na tabbatar da mun basu kariya da rayuwa mai inganci, kana mu kare su daga mumunan cin zarafi.

Wannan shi ne sharhin Muryar Amurka mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.