Accessibility links

Breaking News

Nuna Goyon Baya Ga ‘Yancin Walwalar ‘Yan Jarida


Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken yayin wata ziyara da ya kai Mexico
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken yayin wata ziyara da ya kai Mexico

Sakatare Blinken ya bayyana karara cewa, Amurka za ta ci gaba da ba da goyon baya wajen samun bayanai da kuma kare 'yancin 'yan jarida a duniya.

“Akwai matukar wahala da hatsarin gaske a cikin jarida a duk fadin duniya,” in ji mataimakiyar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka kan Tsaron Farar Hula, Dimokuradiyya, da ‘Yancin Bil Adama Uzra Zeya a wani taron tabbatar da ‘yancin walwalar ‘yan jarida da aka yi a Tallinn, Estonia.

Hadarin da Zeya ta yi magana akai ya bayyana ba da jimawa ba. An kashe Heber Lopez Vasquez, wanda ke ba da rahoto kan cin hanci da rashawa a Mexico a ranar 10 ga Fabrairu.

Muzgunawa iri-iri da ake yi wa ‘yan jarida da kuma rufe gidajen jaridu masu zaman kansu a duniya ya zama ruwan dare. Kasashe 21 daga Kungiyar Hadin gwiwar 'Yancin Kafafen Yada Labarai kwanan nan sun bayyana "damuwa sosai" kan hare-haren da hukumomin Hong Kong da na PRC ke kaiwa kan kafofin yada labarai masu zaman kansu.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya lura cewa, daga 2016-2021, kusan kashi 85% na al'ummar duniya sun ga raguwar 'yancin yada labarai a kasarsu. Wannan, in ji shi, "wani babban abin damuwa ne.

“’Yancin manema labarai na da matukar muhimmanci wajen sanar da jama’a, ba su damar rike gwamnatocinsu, da kuma fito da wasu muhimman batutuwa wadanda idan ba haka ba, ba za su ja hankalin jama’a ba. Mun kuma san abin da ke faruwa idan babu ‘yan jarida: cin hanci da rashawa ya kan bunƙasa; shugabanni marasa kishin kasa suna mulkin kama -karya; sannan ana hana mutane fadin albarkacin baki."

Sakatare Blinken ya ce dole ne tsarin dimokuradiyya ya kai ga kare 'yancin kafofin yada labarai na yanar gizo da wadanda ke aksain hakan. Kasar Amurka ta ƙaddamar da tsare-tsare da dama a yayin taron koli na dimokuradiyya, kamar sabon shirin samar da tallafi ga ‘yan Jarida, da ya hada da horar da su musamman kan fasahar zamani da tsaron kai. Sannan wani sabon shir shi ne, yadda za a yaki da cin zarafi mutane akan kafar yanar gizo.

Har ila yau, Amurka na duban yadda ake amfani da fasahohin zamani wajen kaikaitar 'yan jarida. Ta hanyar sabon taron koli na kula da fitar da dimokuradiyya da yunƙurin kare haƙƙin ɗan adam, Amurka tare da wasu ƙasashe da dama, suna haɓaka ƙa'idar aikin sa kai don yin amfani da matakan sarrafa fitar da kayayyaki don magance yaduwar fasahohin da za a iya amfani da su don cin zarafin 'yan jarida da murkushe 'yan adawa.

Bugu da kari, sakataren ya bayyana shawarwarin da babban kwamitin kwararru kan harkokin shari'a kan 'yancin yada labarai ya bayar, wanda ke ba da shawarar hadin gwiwar 'yancin kafofin watsa labaru da abokan huldarta kan yadda za a mayar da martani yayin da ake kai wa 'yan jarida hari, tare da bayar da shawarwarin daukar matakan takunkumi, kwatankwacin wadanda Amurka ta shigar da kara bayan kisan dan jarida Jamal Khashoggi.

Sakatare Blinken ya bayyana karara cewa, Amurka za ta ci gaba da ba da goyon baya wajen samun bayanai da kuma kare 'yancin 'yan jarida a duniya.

XS
SM
MD
LG