Accessibility links

Breaking News

Amurka Na Goyon Bayan Gudunmowar Da Taiwan Ke Bayarwa A Majalisar Dinkin Duniya


Havana Syndrome
Havana Syndrome

Muna daga cikin kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da dama da ke kallon Taiwan a matsayin amintacciyar abokiyar hulda."

Amurka na goyon bayan muhimmiyar gudunmowar da Taiwan ke bayarwa a Majalisar Dinkin Duniya.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana dalilin da ya sa "Taiwan," in ji shi a cikin wata rubutacciyar sanarwa, "ta zama labarin nasarar demokradiyya.

Tsarinsa yana goyan bayan fayyace, mutunta haƙƙin ɗan adam, da bin doka - ƙimar da ta yi daidai da na Majalisar Dinkin Duniya. Taiwan na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya musamman a fannin fasahar zamani da kuma cibiyar tafiye-tafiye, al'adu, da ilimi.

"Muna daga cikin kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da dama da ke kallon Taiwan a matsayin amintacciyar abokiyar hulda."

Amurka na goyon bayan tsarin da ya dace, wanda zai ba da damar al'ummomin duniya da kuma Majalisar Dinkin Duniya da kanta su ci gajiyar basirar Taiwan da kuma niyar taimakawa. Taiwan ita ce jagora wajen bunkasa fasahohin da za su tsara makomar ba kawai ta tattalin arzikinmu ba, har ma da gwamnatoci da al'ummominmu.

Duniya na buƙatar ƙwarewar Taiwan don taimakawa wajen shimfida ƙa'idodi da tsara makoma wacce fasaha za ta yi amfani, ba ta raunana tsarain dimokradiyya da ‘yancin walwalar dan adam.

"China daya". Daidai da waccan manufar, Amurka tana da dangantaka ta yau da kullun da Taiwan wacce ta yi daidai da dokar yin hulda da Taiwan take bi.

Kamar yadda sakatare Blinken ya bayyana, a mafi yawan shekaru 50 da suka gabata, Taiwan ta taka muhimmiyar rawa a wasu hukumomi na musamman na Majalisar Dinkin Duniya. Duk da haka, a kwanan nan, ba a ba wa Taiwan izinin ba da gudummawa a ayyukan da Majalisar Dinkin Duniya take yi ba.

Sakatare Blinken ya ce "Duk da dubun-dubatar fasinjojin da ke tafiya a duk shekara ta filayen jirgin samanta, Taiwan ba ta da wakilci a Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya." Ya kara da cewa, "Duk da cewa muna da abubuwa da yawa da za mu koya daga matakin da Taiwan ta dauka game da cutar ta COVID-19," in ji shi, "Taiwan ba ta cikin taron hukumar lafiya ta duniya WHO.

Membobin ƙungiyoyin fararen hula daga sassan duniya na shiga ayyukan daban-daban a Majlisar Dinkin Duniya, amma masana kimiyyar Taiwan, ƙwararru a fannin fasaha, 'yan kasuwa, masu fasaha, malamai, ɗalibai, masu fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, da sauransu an hana su shiga cikin waɗannan ayyukan kawai saboda fasfo din da suke rike da su."

Sakatare Blinken ya bayyana cewa, "Mayar da Taiwan saniyar ware, yana lalata muhimman ayyukan Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin da ke da alaƙa, waɗanda dukkansu suna da fa'ida sosai daga gudummawar da take bayarwa.

Don haka ne muke ba wa dukkan kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya kwarin gwiwa da su hada kai da mu wajen goyon bayan Taiwan, mai ma'ana a cikin tsarin Majalisar Dinkin Duniya da ma al'ummar duniya baki daya, daidai da manufarmu ta 'Kasar china daya', wadda ke karkashin dokar huldar Taiwan, ta uku ta haɗin gwiwa."

XS
SM
MD
LG