Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fitar da sanarwar nuna goyon baya ga al'ummar kasar Burma yayin da suke bikin ranar samun 'yancin kai a ranar 4 ga watan Janairu.
"Muna girmama al'ummar Burma da ke kokarin maido da tafarkin dimokuradiyya, mutunta 'yancin bil adama, da bin doka da oda ga dukkan mutanen kasar," a cewarsa.
"Amurka za ta ci gaba da nuna goyon baya ga al'ummar Burma, wadanda ba za su fasa rike fatarsu ba don samun kyakkyawar makoma, duk da cewa gwamnatin kasar na cin zarafinsu."
Rikice-rikicen gwamnatin ya ci gaba tun bayan da sojojin Burma suka kwace ikon gwamnatin Burma a wani juyin mulki a ranar 1 ga Fabrairu, 2021, inda suka tsige tsoffin shugabannin kasar mashawarcin gwamnati Aung San Suu Kyi, da shugaban kasa Win Myint, da 'yan jam'iyyarsu ta siyasa na kungiyar National League for Democracy, wacce ta samu gagarumin rinjaye a babban zaben watan Nuwamba na 2020.
Tun bayan juyin mulkin dai, gwamnatin kasar ta daure mutum 10,000 sannan kuma aka kashe akalla 1,300 ciki har da kananan yara da dama.
A ranar 24 ga watan Disamba, jami'an tsaron gwamnatin sun aikata wani mummunan aiki mai ban tsoro a jihar Kayah. Sojojin Burma sun kashe tare da kona akalla mutane 35 da suka hada da mata, yara, da ma’aikatan kungiyoyin agaji na kasa da kasa, ciki har da biyu daga kungiyar Save the Children.
An gano gawarwakinsu da aka kone a ranar Kirsimeti. Lamarin ya janyo kakkausar suka daga sassan duniya, ciki har da mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wadanda suka yi Allah wadai da kisan tare da "nanata bukatar tabbatar an hukunta duk wadanda suke da alhakin wannan lamarin."
Abin takaici shi ne, gwamnatin na ci gaba da tafka munanan al'amura. Sojojin sun yi luguden wuta kan masu zanga-zangar lumana; sun kona gidaje; an sace da kuma kashe yara; cin zarafi da cin zarafi ta hanyar jima'i a kan fursunonin; tare da kona kauyuka baki daya.
A wata sanarwa ta daban da ya fitar bayan harin jajibirin Kirsimeti a jihar Kayah, Sakatare Blinken ya ce, "ba za a amince da harin da ake kai wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma masu aikin jin kai, kuma irin ta'asar da sojoji ke yi wa al'ummar Burma na nuna dole ne a gaggauta hukunta mambobinta da ke da hannu.”
.Sakatare Blinken ya bayyana cewa, tun daga ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 2021, Amurka ta kakaba wa shugabanin sojojin kasar ta Burma takunkumin karya tattalin arziki, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su kara kaimi wajen hana aukuwar zalunci a kasar ta Burma.
A cikin jawabinsa na bikin ranar ‘yancin kai na Burma, Sakatare Blinken ya yi kira ga gwamnatin soja da ta daina tashe-tashen hankula nan take, ta saki duk wadanda ake tsare da su ba bisa ka’ida ba, sannan su maido da turbar Burma zuwa ga dimokiradiyya ta gaskiya.