Accessibility links

Breaking News

SHARHIN MURYAR AMURKA: Tsai Da Laifukan Illanta Halittu Da Yanayi


Duniyarmu
Duniyarmu

Wannan karon sharhin Muryar Amurka, mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka, ya mai da hankali ne kan yadda ake aikata laifuka masu nasaba da illanta tsarin rayuwar halittu

Laifukan wofinta yanayi – kamar sare itatuwa barkatai, hakar ma'adinai ba bisa ka’ida ba, safarar namun daji, canza dalilin ƙasa , da ayyukan laifuka masu alaƙa, da laifuka masu nasaba da kamun kifi - suna cutar da mutane kuma suna illa ga maudu’in da aka sa gaba, da kuma amfani da duniyarmu ta hanya mai dorewa.

Laifukan wofinta yanayi babbar harka ce ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka a duniya. Yana matukar kawo riba, yana kawo ɗaruruwan biliyoyin daloli a kowace shekara. Har ila yau, yana da matuƙar barna, da lalata abin zaman garin jama’a da albarkatun ƙasa, da yaɗa cututtuka, da lalata muhalli da kuma tura nau’o’in halittu zuwa gaɓar halaka. Kuma yana da nasaba da safarar mutane, muggan kwayoyi da bindigu da almubazzaranci da rashawa, da almundahana, da zamba.

A karshen watan Satumba, Ministan yanayi da muhalli na kasar Norway Espen Barth Eide da Mataimakiyar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka mai kula da teku da muhalli da kimiyya, Monica Medina, su ka shirya wani taro wanda ministoci da manyan jami'ai daga kasashe goma sha daya suka halarta. Masu shirya taron haɗin gwiwar biyu sun yi amfani da taron don sake nazarin tsarin hada kai wajen yakar laifukan na wofinta yanayi.

"Wadannan laifuffuka suna illa ga zaman tare na halittu na muhallinsu, suna kawo cikas ga ci gaba kuma suna haifar da gagarumin sakamako na dogon lokaci ga al'ummomi masu zuwa," in ji Minista Eide da Mataimakiyar Sakatare Medina a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron. Kodayake daidaikun laifuffuka da su ka danganci wofinta muhalli tuni su ka haramtu, kuma ana tuhumar su a yawancin ƙasashe, waɗannan matakan galibi ba a kintse su ke ba, kuma ba su isa su lalata waɗannan hanyoyin sadarwa na laifi ba. Kasar Amurka da Norway, suna fatan ganin hadin kai wajen yakar Laifukan Wofinta Halittu zai yi tasiri don tayar da ra'ayin siyasa, da kuma ƙaddamar da kudi; don shiga ƙungiyoyin jama'a, ƙwararrun, da tilasta bin doka; don ƙarfafa ƙarfin aiki don yaƙar laifukan yanayi; da kuma tallafa wa haƙƙi da tsaro na ‘ƴan asalin ƙasar da al'ummomin yankin. “Wadannan ayyukan aikata laifuka suna barazana ga tsaron ƙasa, suna lalata tsarin doka, da wawashe albarkatun ƙasa da kudaden shiga da karar da wasu na’ukan dabbobi kwata kwata, da yada cutattuka. Dole ne a dakatar da su kuma lokacin daukar mataki ya yi,” in ji Mataimakiyar Sakatariya Madina.

“Kungiyoyin da ke aikata wadannan laifuffuka suna kara rura wutar cin hanci da rashawa, laifukan da su ka shafi kudi da suka hada da kauce wa biyan haraji da halasta kudaden haram, da shuka barna a duk inda suke. Babu kasa, babu yanki, babu ruwa, babu mutanen da suka tsira daga haramtattun ayyukansu, sau da yawa da munanan ayyukansu. Muna sa ran yin aiki tare da waɗanda suka haɗa mu a yau yayin da muke ƙara haɓaka sabon shirin haɗin gwiwa – Hadin Kai Don Yakar Laifukan Wofinta muhalli. "

An karanta sharhin Muryar Amurka mai bayyana ra’arin Gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG