Yakin Sudan Na Haifar Da Matsananciyar Yunwa

Wata mata rike da danta a wani sansanin 'yan gudun hijira

Amurka na kira ga Janar Abdel Fattah al-Burhan da Hemedti da su halarci tattaunawar tsagaita bude wuta a Switzerland a ranar 14 ga watan Agusta.

Sudan na cikin wani mawuyacin hali saboda "wannan yaki na rashin hankali," in ji Ambasada Robert Wood, madadin wakili na musamman kan harkokin siyasa, ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

“An bayyana matsananciyar yunwa a hukumance a sansanin ‘yan gudun hijira na Zamzam da ke yankin El Fasher na Arewacin Darfur, inda sama da mutum 500,000 ke samun mafaka. Masana suna zargin ana cikin yunwa har a sansanonin 'yan gudun hijira na Abu Shouk da Al Salam da ke kusa."

“Iyalan da suka tsere daga mummunan tashin hankali sun shafe watanni suna fama da yunwa. Yara suna cin datti da ganye. Kuma a kowace rana, jarirai na fama da yunwa,” in ji Ambasada Wood. Amma duk da haka, duk da cewa ana samun taimakon jin kai, Sojojin Sudan, ko SAF, da Rundunar Rapid Support Forces, ko RSF, sun zaɓi barin mutanen Sudan su shiga cikin yunwa ta hanyar toshe hanyoyin jin kai:

"Wannan ya hada da SAF da ke hana masu ba da agajin gaggawa ta hanyar tsallakawa kan iyakar Adré, wanda ke da sa'o'i kawai daga Zamzam Camp. Kamar dai yadda suka toshe hanyar kai agaji daga Adré da furuci guda ɗaya. Amma kuma SAF da gwamnatin Port Sudan za su iya kawo karshen wannan cikas a yau."

A cewar kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders, akwai isasshen abinci kawai ne don kula da yara masu fama da tamowa a sansanin Zamzam na tsawon mako biyu. Kungiyar Doctors Without Borders ta ce adadin yaran da ke karbar wannan agaji ya ragu, saboda RSF sun toshe manyan motocin dakon kaya.

Ambasada Wood ya ce "Tun da aka fara wannan rikici, Amurka ta yi kira ga kasashen duniya da su kara kulawa, su ba da kari, da kuma kara kaimi." Misali Amurka ta jagoranci bayar da taimakon sama da dala biliyan 1.6 ga Sudan da kasashe makwabta tun bayan barkewar rikicin a shekarar 2023.

"Amma a yanzu, RSF da SAF dole ne su cire shinge don a ci gaba da ba da taimako da ba da damar abinci, ruwa, da magunguna da ake buƙata su gudana cikin 'yanci kuma a wuraren shiga da yawa, ta kan iyakoki da layin rikici. Dole ne su kuma taka rawar gani a tattaunawar tsagaita bude wuta.”

Amurka na kira ga Janar Abdel Fattah al-Burhan da Hemedti da su halarci tattaunawar tsagaita bude wuta a Switzerland a ranar 14 ga watan Agusta.

Ambasada Wood ya ce "Babu wata hanya mafita ta soji kan wannan yaki." “Ana auna kawai yawan asarar rayukan fararen hula, da korar miliyoyin mutane daga gidajensu; rashin abinci mai gina jiki mai tsanani; fyade, azabtarwa, da sauran musgunawa; da kuma kisan kare dangi.”

Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.