Accessibility links

Breaking News

Blinken A Babban Taron Shirin Samar Da Abinci Na Duniya


"Feed the Future" shiri ne da Gwamnatin Amurka ta bullo da shi don yakar bala'in yunwa da kuma samar da abinci a duniya (Photo: USAID)
"Feed the Future" shiri ne da Gwamnatin Amurka ta bullo da shi don yakar bala'in yunwa da kuma samar da abinci a duniya (Photo: USAID)

Wannan karon Sharhin Muryar Amurka ya tabo batun samar da abinci a duniya, muhimmancin hakan, da kuma yadda ya kamata a yi hakan.

Mutane fiye da miliyan 200 a duniya na fama da matsananciyar karancin abinci, in ji sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken a wajen babban taron tabbatar da samuwar abinci a duniya na baya-bayan nan.

A watan Mayu, Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da Jadawalin Tsarin Samar Da Abinci a Duniya: Matakan da ya kamata a dauka. Ta yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da su dauki matakai guda bakwai, wadanda suka hada da bude kasuwannin abinci da na noma, da kara samar da taki, da saka hannun jari a fannin noma mai jure canjin yanayi.

Kasashe fiye da 100 ne suka rattaba hannu kan jadawalin, kuma da yawa sun fara aiki kan wadannan kudurorin. "Aikin yana da mahimmanci," in ji Sakatare Blinken, "saboda rikicin da ake ciki yanzu shine wanda babu wata ƙasa ko ma ƙungiyar ƙasashe da za ta iya magancewa ita kaɗai." A babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Shugaba Biden ya ba da sanarwar ware sama da dala biliyan 2.9 a wani sabon tallafi don magance matsalar karancin abinci a duniya, tare da dorawa kan tallafin dala biliyan 6.9 a Amurka don tallafa wa shirin samar da abinci na duniya da aka riga aka yi kudurinsa a wannan shekarar.

Amma ba kowa ne ke ba da gudummawa ba, in ji Sakatare Blinken. “Wasu kasashen da ke da karfin tabukawa da yawa suna cikin wadanda ke bayar da kalilan. Dole a canza lale. Kuma ko mene ne kasashen suka yi ya zuwa yanzu, ana kira ga kowace kasa da ta kara yi da yawa.”

"Wata hanya kuma da za mu iya tallafa wa agajin gaggawa ita ce ta ingiza tsawaita yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya suka taimaka aka kulla tsakanin Rasha da Ukraine, wadda ta ba da damar fitar da hatsi da sauran kayayyakin amfanin gona daga tashoshin jiragen ruwa na Bahar Rum," in ji Sakatare Blinken.

Mataki na biyu shi ne taimaka wa kasashe su bunkasa karfin samar da abincinsu, a cewar Sakatare Blinken.

A cikin shekaru biyar masu zuwa, Amurka za ta yi aiki tare da Majalisar Dokokinmu don zuba kudi fiye da dala biliyan 11 a duk duniya don wannan burin na samar da amfanin gona mai dorewa. A watan da ya gabata, mun ƙara shigar da sabbin abokan hulɗa daga Afirka guda takwas a shirin nan mai lakabin Ciyar Da Gobe. Wannan shirin namu na kwatance ne don faɗaɗa hanyoyin kare lafiyar jama'a, don ƙarfafa tsarin abinci, don haɓaka abinci mai gina jiki.

A ƙarshe, akwai buƙatar samun kwakkwaran haɗin kai tsakanin gwamnatoci, ƙungiyoyin yanki, gidauniyoyi, da ƙungiyoyin sa-kai don tabbatar da cewa suna aiki tare.

Amma watakila mafi mahimmanci, fiye da abin da muke faɗa, shi ne, ba shakka, abin da muke yi," in ji Sakatare Blinken. "Lafiya, kwanciyar hankali, [da] jin daɗin jama'armu ya dogara ne da tsarin tabbatar da wadatar abinci da muke ginawa tare."

Wannan shi ne sharhin Muryar Amurka, mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG