Accessibility links

Breaking News

Alamomin Samun Cigaba A Tigray


Firaministan Habasha Abiy Ahmed
Firaministan Habasha Abiy Ahmed

A watan Nuwamban da ya gabata, bangarori biyu a mummunan tashin hankalin da aka kwashe shekaru biyu ana yi, wato Tigray People’s Liberation Front, ko TPLF, da gwamnatin Habasha, sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin.

Yarjejeniyar ta yi kiran da a dawo da tallafin jinkai ba tare da tsangwama ba da ke kunshe da cikakken tsarin adalci na rikon kwarya na kasa.

Kungiyar ta TPLF ta mika manyan makamanta da yawa da suka hada da tankunan yaki da rokoki ga kungiyar Tarayyar Afirka yayin da gwamnatin Habasha ta kyale kayan agajin da ke kwarara cikin yankin na Tigray.

Dakarun na Eritrea sun fara janyewa daga garuruwa da wuraren da suka mamaye a yankin na Tigray na tsawon watanni tare da komawa kan iyakar kasar zuwa Eritrea.

"Muna yaba da ci gaba da aiwatar da muhimman abubuwa na dakatar da yarjejeniyar yaki da kuma rawar da kungiyar sa ido ta hadin gwiwa ta AU ta taka."

“Muna sane da cewa sojojin Eritrea sun fara janyewa daga Habasha. Muna sake jaddada kiran da ya fito daga tattaunawar da ake yi a Afirka ta Kudu, na janye dukkan dakarun kasashen waje."

"Ficewar Eritriya da sauran dakarun na da mahimmanci don samun dawwamammen zaman lafiya, samar da cikakkiyar damar jinkai, da kuma tabbatar da diyaucin Habasha."

Akwai sauran aiki, amma ci gaban na nuna alamun nasara kuma yana bai wa al’ummar Habasha karfin gwiwa.

XS
SM
MD
LG