Accessibility links

Breaking News

Kare Doka Da Oda


FILE - The International Criminal Court, or ICC, is seen in The Hague, Netherlands, Nov. 7, 2019.
FILE - The International Criminal Court, or ICC, is seen in The Hague, Netherlands, Nov. 7, 2019.

Wannan karon Sharhin Muryar Amurka ya tabo batun mutunta doka da oda ne a matakin kasa da kasa

Ka'idar bin doka da oda ta ba da umurni cewa dukkan mutane, cibiyoyi da hukumomi, jama'a da masu zaman kansu su kasance wadanda za a iya hukunta su a gaban kotu.

Tsarin dokar yana kare marasa karfi.

Yana hana wariya, da cin zarafi, yana ƙarfafa amincewa da yadda ga cibiyoyi da ƙungiyoyi, da kwarin gwina haɗin kan al’umma.

"Babu wani mutum, ko Firayim Minista ko shugaban kasa; babu wata kasa da ta fi karfin doka,"

"Wannan alƙawari ne mai ƙarfi ga Amurka da kuma ƙa'idar Majalisar Dinkin Duniya."

"A yau, wasu kasashe suna nuna gazawa a cikin sadaukarwarsu ga ka'idodin Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya."

"A Rasha, a DPRK, a Iran, a Nicaragua, da kuma Siriya, rahotanni masu ban tsoro suna bayyana dalla-dallar yadda gwamnatoci ke tsarewa, azabtarwa, ko kashe abokan adawar siyasa, ko masu fafutuka, masu kare hakkin bil'adama, ko 'yan jarida."

"Kuma a Burma, Belarus, Cuba, Iran, da Sudan mun ga inda a ke kai hari da cin zarafin masu zanga-zangar lumana."

"Dole ne mu yi hisabi ga duk wadanda ba su mutunta diyaucin kasa ba, ko suka taka 'yancin ɗan adam."

"Za mu ci gaba da yin komai -- duk abin da za mu iya yi don tabbatar da mutunta 'yancin ɗan adam da bin doka a kowane mataki."

XS
SM
MD
LG