Accessibility links

Breaking News

WANI MATAKI NA TAKE HAKKIN YAN NICARAGUANS


Daniel Ortega
Daniel Ortega

Amurka ta yi Allah wadai da shawarar da gwamnatin Nicaragua ta yanke na kwace wa 'yan kasar 94 ‘yancinsu na zama 'yan kasarta da kuma soke zama 'yan kasar fursunonin siyasa 222 da aka sako daga gidan yari.

"Wadannan ayyukan ba su dace da Dokar Haƙƙin Dan Adam ta Duniya ba, wadda ta tanadi cewa kowa yana da 'yancin zama ɗan ƙasa."

"Wannan wani mataki ne na koma baya ga al'ummar Nicaragua da kuma karin mataki na tabbatar da mulkin kama karya."

A ranar 9 ga Fabrairu, an saki fursunonin siyasa 222 daga kurkuku aka kai su Amurka.

An tarye su da kayan kulawa da lafiyar jiki da tare da taimako ta fannin shari'a.

A Nicaragua, Shugaba Daniel Ortega ya yi wa fursunonin siyasar da aka saki lakabi da "'yan ta'adda."

Wani alkali ya ce sun aikata laifin yin zagon kasa ma ’yancin kasar Nicaragua da kuma diyaucinta; an kuma “mai da su.”

"Suna so su kira gudun hijirar a matsayin kora, wanda ba bisa ka'ida ba ne kuma an haramta shi bisa ka'idojin kare hakkin bil'adama na duniya."

Shawarar kwace ‘yan zama dan ƙasa ko zama ɗan ƙasa daga mutanen Nicaragua, waɗanda ke neman yin amfani da muhimman haƙƙoƙin ɗan adam abu ne mai muni.

"Muna ci gaba da jajircewa wajen karfafa karin matakan ga gwamnatin Nicaragua ta dauka na maido da 'yancin jama'a, musamman ma dangane da shawarar da suka yanke na sakin fursunonin siyasa 222."

"Wannan yunkurin... mataki ne da ya saba ma hakan."

XS
SM
MD
LG