A wannan shekarar da ta gabata, tun daga farkon cikakkiyar mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a watan Fabrairun 2022, ta bijiro da wasu munanan ayyukan take hakkin bil Adama da dokokin jinkai na kasa da kasa da Tarayyar Rasha ta yi a matsayin wani bangare na yakin da take yi da Ukraine.
"Kada ku yi kuskuren fahimta, ta’asar na gefe daya," in ji tsohon jakadan Amurka a Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam a Geneva, Keith Harper, mai gudanar da wani babban taro a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya kan munanan ayyukan take hakkin bil'adama da cin zarafi da Rasha take yi wa Ukraine.
"Amurka ta yi imanin cewa sojojin Rasha sun aikata laifukan cin zarafin bil'adama a Ukraine," in ji wakiliyar Amurka ta dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfields. “Shaidar nada matukar yawa.”
“Hukumar bincike ta kasa da kasa mai zaman kanta kan Ukraine… da kuma tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido kan hakkin bil adama a Ukraine, sun tattara tarin laifuka da sauran cin zarafi da sojojin Rasha suka yi.
Hukuncin kisa ba shari’a. Kulle jama’a ba bisa ka'ida ba. Azabtarwa, fyade, da sauran nau'ikan cin zarafin jinsi da cin zarafin jima'i. Kuma mun san mata, yara, tsofaffi, nakasassu, da sauran marasa galihu da aka ware sun fi fuskantar wadannan hare-hare."
“Rahotanni masu sahihanci sun nuna cewa jami’an Rasha sun shirya canja wuri, kaura, sake koyo, riko, ko kuma tilasta rikon dubban yara. Wasu daga cikin wadannan yara sun zama marayu a wannan yakin. Kuma wasu sun riga sun zauna a cibiyoyi masu tsananin bukatun kiwon lafiya, ”in ji Jakadiya Thomas-Greenfield.
“A yawancin lokuta, iyaye suna aika yara zuwa wuraren da suke tunanin ‘sansanin rani’ don kare lafiyar ’ya’yansu amma sai aka hana su tuntubar su da kuma sake haduwa da ’ya’yansu. A wasu lokuta, iyaye sun ki aika ‘ya’yansu zuwa ‘sansanoni’ na Rasha, kuma hukumomin mamaya na Rasha sun renon su ko ta halin kaka.
Kuma bari mu fayyace komai: wannan ba wani aiki ne na bngaren mamayar ba. Muna da shaidar cewa Shugaba Putin da Kremlin sun himmatu wajen yunkuri hanawa da murkushe asalin Ukraine, tarihinsu, da al'adunsu.”
Jakadiya Thomas-Greenfield ta ce "Ku kuma sa ido a kan maganata." "Za a dauki mataki kan ta'asar Rasha."
“Amma a yanzu, babban abin da mutanen Ukraine ke bukata shi ne zaman lafiya. Kamar yadda shugaba Biden ya fada a ziyarar da ya kai Kyiv a wannan makon, ‘Shugaba Putin ya zabi wannan yaki. Duk ranar da ake ci gaba da yakin shine zabinsa.”
"Sakonmu ga Shugaba Putin shi ne: Kawo karshen wannan yakin. Kawo karshen zalunci. Ka dakatar da ukubar da sojojinku suka jefa Ukraine da kuma duniya a ciki. Amma kafin wannan ranar ta zo, dole ne dukkanmu mu tsaya tare da Ukraine,” in ji Jakadiya Thomas-Greenfield. "Kuma dole ne dukkanmu mu tsaya tsayin daka kan daukar mataki a kan cin zarafin bil'adama."
Wannan shi ne sharhin Muryar Amurka mai bayyana ra'ayin gwamnatin Amurka.