Accessibility links

Breaking News

Babbar Ajandar G20


G20-INDIA/
G20-INDIA/

Yanzu sai sharhin Muryar Amurka wanda zai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka:

Taken taron kungiyar kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki ta G20 na bana, wanda aka kammala kwanan nan a New Delhi, shi ne "Duniya Daya. Iyali Daya. Makoma daya."

A wani taron manema labarai a karshen taron, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yaba wa Indiya, wacce a halin yanzu ke rike da shugabancin kungiyar ta G20, saboda "ajandar da suke neman cimma."

Wannan ajandar ta mayar da hankali ne kan warware wasu muhimman kalubalen da duniya ke fuskanta, da suka hada da samar da abinci, kiwon lafiya a duniya, yaduwa da safarar miyagun kwayoyi, sauyin makamashi, sauyin yanayi da hasarar albarkatun halittu, da kuma batun shingayen dake hana mata shiga harkokin tattalin arziki.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken

Hanyar tinkarar wadannan kalubalolin ita ce yin aiki tare. Game da batun haramtattun magunguna, misali, Sakatare Blinken ya ce, “Ba wata kasa da za ta iya magance wannan matsalar ita kadai. Katse hanyoyin samar da abubuwan ga wadannan mutane, da hana karkatar da magunugna da doka ta amince da su zuwa ga masu amfani dasu ba bisa ka'ida ba, da wargaza kungiyoyin masu aikata laifuka na kasa da kasa wadanda ke haifar da cin hanci da rashawa da cin gajiyar wahalar wasu, wadannan kalubaloli ne da ke bukatar hadin gwiwa da kokarin duniya."

Ya fada a taron G20 da kuma wasu tarurrukan baya-bayan nan cewa, “kasashe suna son yin hadin gwiwa da Amurka, saboda suna ganin mun fito don warware matsalolin da muke fuskanta tare, da samar da ci gaban tattalin arziki na bai daya, da saka hannun jari a gwagwarmayar tsakaninmu, da kuma tsayawa tsayin daka kan kare dokokin kasa da kasa ta hanyoyin da za su amfanar da dukkan kasashe, gami da ‘yancin kowace kasa ta zabi hanyarta, ba tare da tashin hankali, tilastawa, da barazana ba.”

Sakatare Blinken ya yaba wa fadar shugaban Indiya da Ministan Harkokin Wajen Indiya Subrahmanyam Jaishankar saboda samun amincewar G20 kan batutuwa da dama, wanda aka nuna a cikin kundin takaitaccen bayanin shugabanci kan sakamakon taron, dake zama na farko ga ministocin harkokin wajen G20.

Sakatare Blinken ya kuma bayyana rashin jin dadinsa kan yadda kasashe biyu, Rasha da jamhuriyar jama'ar kasar China, ba su shiga yarjejeniyar G20 kan sakin layi biyu da sauran kasashe 18 suka amince da su ba. Wani sashe mai muhimmanci ya bayyana cewa yawancin membobin "sun yi Allah wadai da yakin da ake yi a Ukraine kuma sun jaddada cewa yana haifar da wahala mai yawa da kuma kara dagula al’amura da ake samu a tattalin arzikin duniya." Sauran ya sake tabbatar da cewa yana da matukar muhimmanci a kiyaye dokokin kasa da kasa da bin tsarin hadin kan kasashe duniya da ke kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sakatare Blinken ya bayyana cewa, "Banda abin da Rasha ke yi, mun nuna a nan Delhi abin da za mu yi: wato ba da sakamako kan matsalolin da suka fi shafar rayuwar mutanenmu. Ya kara da cewa, masu masaukin mu, sun himmatu wajen yin hakan a tsawon lokacin shugabancin su na G20. A kan haka da kuma jagorancinsu da karimcinsu, "[Ina bayyana] godiyata ga Indiya."

Wannan shine Muryar Amurka da ya bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG