Accessibility links

Breaking News

A hukumance Amurka ta gamsu cewa an yi juyin mulkin soja a Nijar.



Shugaban majalisar mulkin sojin jamhuriyar Nijer Janar Abdourahamane Tchinai
Shugaban majalisar mulkin sojin jamhuriyar Nijer Janar Abdourahamane Tchinai

Rubutacciyar sanarwar da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Matthew Miller, ya fitar ta zo ne sama da watanni biyu, bayan da shugabannin sojoji a Nijar suka hambarar da zababben shugaban kasar, Mohammed Bazoum, a ranar 26 ga watan Yuli, tare da yi masa daurin talala. A cikin tsaka mai wuya, Amurka ta yi kokarin shawo kan shugabannin sojojin Nijar da su dawo da tsarin mulkin kasar, da sakin shugaba Bazoum, da mayar da shi kan karagar mulki.Yunkurin da bai yi nasara ba ya zo ne da sakamako ga Nijar, wadda Amurka ta hada kai da su wajen yaki da ta'addancin da ke da alaka da al-Qaida da IS.

Kamar yadda mai magana da yawun Miller ya bayyana, bisa ga dokar kasafi na shekara-shekara na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, Amurka dole ta dakatar da yawancin taimakon da ta ke baiwa gwamnatin Nijar. Wannan ya hada da dala miliyan 200 a wasu shirye-shirye na taimakon kasashen waje, wanda Amurka ta dakatar da wani dan lokaci a ranar 5 ga watan Agusta. Bugu da kari kuma, an dakatar da tallafin shirin Millennium
Challenge ke baiwa Nijar, ciki har da duk wani aikin shirye-shirye kan Yarjejeniyar Sufuri na Yankin Neja da dala miliyan 302 da duk wani sabon aiki na yarjejeniyar 2018.

Ko da yake a halin yanzu har yanzu Amurka na da sojoji a Nijar, amma a halin yanzu ayyukan sojojin Amurka sun takaita ne ga ayyukan leken asiri da sa ido da kuma bincike don kare lafiyar ma'aikatan Amurka. An dakatar da ayyukan yaki da ta'addanci da kuma horar da sojojin Nijar.

Kakakin Miller ya jaddada, duk da haka, Amurka “za ta ci gaba da kula da taimakon jin kai, abinci, da kiwon lafiya na ceton rai don amfanin al’ummar Nijar. Har ila yau, Amurka na da aniyar ci gaba da yin aiki tare da gwamnatocin yankin, ciki har da na Nijar, wajen ciyar da moriyar juna a yammacin Afirka."

"Muna tare da al'ummar Nijar a cikin burinsu na tabbatar da dimokuradiyya, wadata da kwanciyar hankali," in ji kakaki Miller. "Tun bayan juyin mulkin, mun goyi bayan kokarin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka na yin aiki tare da Nijar don samun nasarar komawa kan mulkin dimokuradiyya."

Ya kara da cewa duk wani ci gaba da taimakon Amurka zai bukaci daukar mataki daga hukumar mulkin soji, Majalisar Tsaro ta Kasa, "don shigar da mulkin dimokiradiyya cikin sauri da ingantaccen lokaci."

A wani jawabi na baya-bayan nan a Angola, sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya yi gargadin cewa, "Lokacin da janar-janar suka yi watsi da ra'ayin jama'a, suka kuma fifita burinsu fiye da bin doka da oda, tsaro yana shan wahala - kuma dimokradiyya ta na mutuwa."

Ya kamata a maido da mulkin dimokradiyya a Nijar.

Anncr: Sharhin Muryar Amurka kenan mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka

XS
SM
MD
LG