Accessibility links

Breaking News

Kungiyar G7 Ta Gargadi Iran


Blinken
Blinken

Amurka da kawayenta na kungiyar G7 sun gargadi Iran da kada ta tura makamai masu linzami wa Rasha. A cikin wata sanarwa da suka bayar, shugabannin kungiyar da suka hada da Amurka, Canada, Faransa, Japan, Italiya, Jamus, da kuma Burtaniya, sun ce "sun damu matuka cewa Iran na tunanin mika fasahar ballistic ga Rasha bayan ta mika wa gwamnatin Rashar da UAVs [jirage marasa matuka], waɗanda ake amfani da su wajen kai hare-hare kan fararen hula a Ukraine."

A wani taron manema labarai, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, John Kirby, ya karanta takardar sanarwar da cewa:

"Bari in karanta ma ku: "Idan Iran za ta ci gaba da samar da makamai samfurin ballistic ko wata fasaha mai alaka da hakan ga Rasha, a shirye mu ke mu mayar da martani cikin sauri, kuma a ta hanyar da ta dace, gami da sabbin matakai masu mahimmanci a kan Iran."

Mashawarci Kirby ya bayyana cewa, banda jirage marasa matuka da gwamnatin Iran ta samar wa kasar Rasha, har ma da samar da kayayyakin da za su bai wa Rasha damar kera su a kasar Rashar. An yi amfani da jirage marasa matuka wajen kai hare hare kan fararen hula da madafun ci gaban Ukraine; tura makamai samfurin ballistic zai zama babbar rurutawa.

“Wannan huldar tsaro ce mai karuwa wacce muke sa ido a kai sosai-sosai. ... Muna so mu jaddada karara, ga Iran da Rasha cewa za su gamu da sakamako cikin sauri muddun su ka yi hakan."

Mai ba da shawara Kirby ya yi nuni da cewa dangantakar tsaro tsakanin Iran da Rasha ba wai kawai za ta yi illa ga al'ummar Ukraine ba ne, har ma da mutanen yankin Gabas ta Tsakiya, saboda ita ma Iran na sa ran samun wani abu daga ciki. Ba wai kawai game da sayar da makamai samfurin ballistic ma Rasha ba. Su ma kansu [Shugabannin Iran] na sa ran samun fasahar sojin Rasha don amfanar kansu."

Da yake magana game da samar ma Rasha makamai samfurin balistic da Iran ka yi, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana cewa, "Mun aike da sako karara ga Iran cewa kada ta yi hakan.”

XS
SM
MD
LG