Accessibility links

Breaking News

BUKATAR GAGGAUTA SAMAR DA ZAMAN LAFIYA A SUDAN


US Blinken Texas
US Blinken Texas

"Maganar gaskiya daya ce kacal a nan, ita ce a ajiye bindigogin." In ji Perriello.

Kusan shekara guda kenan da fada ya barke a Sudan tsakanin Sojojin Sudan, SAF, da kuma kungiyar mayakan sa kai, RSF, wanda ya jefa Sudan cikin yanayin da masu lura da al'amura suka bayyana a matsayin "Jahannama a duniya."

'Yan Sudan miliyan goma sha takwas na fuskantar matsananciyar yunwa, kuma yunwa na kunno kai. Kusan mutane miliyan takwas ne aka tilasta wa barin gidajensu. A watan Disamba, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ƙaddara cewa mambobin SAF da RSF sun aikata laifukan yaki. Ya kuma tabbatar da cewa 'yan kungiyar ta RSF da kungiyoyin mayaka masu alaka sun aikata laifukan cin zarafin bil'adama da kuma kisar kare dangi a Darfur.

Wakilin Amurka na musamman kan Sudan Tom Perriello ya yi bulaguro kwanan nan zuwa Afirka da Gabas ta Tsakiya, inda ya zanta da shugabanni da al'ummar Sudan game da bala'in da ke faruwa a Sudan da kuma bukatar a gaggauta sake kaddamar da tattaunawar sulhu a hukumance:

“Har mun fara ganin alamun matsananciyar yunwa a duk fadin kasar Sudan. Mu na sane da munanan ayyukan cin zarafi, musamman ga mata da yara, tilasta shiga aikin tsaro, har ma da bauta a cikin wannan rikici wanda dole ne a kawo karshensa. Kuma yanzu muna ganin halin da ake ciki yayin da muke shiga lokacin damina wanda zai iya yin muni cikin sauri, kuma har matsalar jinkai ta yi muni."

Wakili na musamman Perriello ya ce, "Maganar gaskiya daya ce kacal a nan, ita ce a ajiye bindigogin." Ya kara da cewa hakan na bukatar manyan hafsan hafsoshin biyu, babban hafsan sojojin SAF Abdel Fattah al-Burhan da shugaban RSF Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, da su cimma matsaya a duk fadin yankin "su hada kai mage da zaman lafiya."

"Mu na buƙatar sake fara tattaunawa a hukumance. Mu na fatan hakan zai faru da zarar an kammala azumin watan Ramadan, wato tattaunawa ce mai kunshe da manyan masu ruwa da tsaki a yankin da kuma manyan muryoyin daga ciki, kuma za mu iya cimma wannan yarjejeniya ba kawai don kawo karshen tashe-tashen hankula ba, amma don mu bude don bada damar cikakken jinkai."

Wakilin na musamman Perriello ya ce ziyarar da ya kai yankin ta bayyana wani sabon yanayi na gaggawa game da Sudan: “Kowa ya fahimci cewa wannan rikicin ya kai matsayin da ya wuce misali. Kuma hakan na nufin kowa ya ajiye duk wasu bambance-bambance a gefe tare da hadin kai wajen ganin an warware wannan rikici.” Mafita, in ji wakili na musamman Perriello, wadda za ta kai ga maida Sudan kasar da al'ummarta za su yanke shawarar makomarsu da kansu."

XS
SM
MD
LG