Accessibility links

Breaking News

Dole A Kare Fararen Hula Da Ma’aikatan Agaji


Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken da Firaministan Isira'ila, Benjamin Netanyahu
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken da Firaministan Isira'ila, Benjamin Netanyahu

A ranar 7 ga watan Afrilu aka cika watanni shida fara rikicin Isra'ila da Falasdinu wanda ya samo asali daga wani mummunan hari da Hamas ta jagoranta kan fararen hulan Isira'ila. A lokaci guda kuma, Hamas ta yi garkuwa da mutane 250 da su ka hada da Isra'ilawa 'yan kasashen waje. Tun daga nan, aka ci gaba da gwabza fada, galibi a Gaza.

Kwashe watanni shida da aka yi ana gwabza fada ya yi sanadin asarar rayukan mutane 1200 a Isira’ila, wadanda su ka hada da Isira’ilawa da ‘yan kasashen waje. A Gaza, sama da mutane 32,000 aka kashe yayin da sama da 75,000 suka jikkata.

Har ila yau fadan ya yi sanadin mutuwar jami'an agaji 224 da ke aikin dakile yunwa a Gaza. Wannan ya hada da mutane bakwai na kungiyar agaji ta World Central Kitchen da suka mutu a ranar 1 ga Afrilu saboda hare-haren da Isra'ila ta kai a kan ayarin motocinsu duk da cewa motar na dauke da alama.

"Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da wajibcin kare ma'aikata," in ji John Kelley, Ministan Harkokin Siyasa na Amurka a Majalisar Dinkin Duniya. Ya kara da cewa, "Abin takaici, ba a bi ka’idojin kariyar ba a Gaza."

"Amurka ta fusata kuma zuciyarta ta karaya" game da mutuwar waɗannan mutane, waɗanda ke ba da abinci ga fararen hula da ke fama da yunwa a tsakiyar yaƙi. Waɗannan ma'aikatan sun kasance jajirtattu kuma marasa son kai."

“Bugu da ƙari, wannan al’amari an sha yin irinsa. Wannan rikici ya kasance daya daga cikin mafiya muni a baya bayan nan, dangane da adadin ma’aikatan agaji da aka kashe,” in ji Ambasada Kelley.

"Kamar yadda Shugaba Biden ya sanar da Firayim Ministan Isra'ila Netanyahu a ranar 4 ga Afrilu, Isra'ila, ya ce, "dole ne" ta yi sanarwar aiwatar da wasu takamammun matakai na musamman, da kuma matakan da za a iya aunawa don magance wahalar da fararen hula ke ciki, wahalar jinkai, da kariyar ma'aikatan agaji." Manufar Amurka game da Gaza za ta kasance ta hanyar matakin da Isra'ila za ta dauka nan take kan wadannan matakan."

"Har ila yau, muna ci gaba da yin duk abin da za mu iya don taimakawa wajen kai agajin jinkai ga fararen hula Falasdinawa a Gaza ta kowace hanya," in ji Ambasada Kelley.

"Amma wadannan ayyukan ba su isa su biya bukatun fararen hula Falasdinawa a Gaza ba. Ana matukar bukatar taimakon jinkai a yanzu, kuma dole ne a saukaka shi don rage tasirin mummunar yunwar da ke tafe. Al'ummar Gaza gaba daya sun san matsanancin karancin abinci. Duk al’ummar Gaza na bukatar agajin jinkai."

Ambasada Kelley ya ce "tsagaita bude wuta nan take na da matukar muhimmanci don daidaitawa da inganta yanayin jinkai da kuma kare rayukan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba." "Mun bukaci Firayim Minista Netanyahu da ya ba wa masu tattaunawarsa damar kulla yarjejeniya ba tare da bata lokaci ba don dawo da wadanda aka yi garkuwa da su gida. Muna kuma kira ga Hamas da ta amince da yarjejeniyar da ke kan teburin."

XS
SM
MD
LG