Accessibility links

Breaking News

Amurka Na Goyon Bayan Tsarin Dimokradiyya A Venezuela


Kakakin ma'aikatar harkokin wajen spokesman Ned Price
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen spokesman Ned Price

Amurka za ta ci gaba da zama mai ba da shawara ga al'ummar Venezuela yayin da suke kokarin ganin an maido da mulkin dimokradiyya cikin lumana ta hanyar zabe mai inganci da adalci.

Amurka ta yi maraba da yarjejeniyar da Majalisar Dokokin kasar Venezuelan da aka zaba ta hanyar dimokradiyya a 2015 ta cimma na tsawaita wa'adinta na tsawon shekara guda, tare da Juan Guaidó a matsayin shugaban rikon kwarya. Amurka na ci gaba da amincewa da ikon Majalisar Dokokin kasa ta 2015 a matsayin cibiyar dimokiradiyya ta ƙarshe da ta rage a Venezuela.

Tsarin mulkin Nicolás Maduro na danniyar siyasa, da cin zarafin bil'adama, da kuma tsauraran takunkumi kan 'yan siyasa da na farar hula da 'yancin fadin albarkacin baki ya tauyewa al'ummar Venezuelan ‘yancin morar alfanun dimokradiyya.

“Muna goyon bayan kokarin. . .tabbatar da tsarin dimokuradiyya da bin doka a Venezuela," in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price a wata sanarwa.

"Muna kira ga Nicolás Maduro da ya sake tattaunawa da Mexico, kuma ya yi hakan cikin aminci don amfanin al'ummar Venezuela," in ji Mista Price. "Za mu ci gaba da yin aiki tare da ɗimbin abokan hulɗa na Venezuela da na duniya ta hanyar amfani da duk hanyar diflomasiyya da tattalin arziki da suka dace don matsa lamba don a saki duk waɗanda ake tsare da su ba bisa ƙa'ida ba saboda dalilai na siyasa, 'yancin kai na jam'iyyun siyasa, mutuncin 'yancin faɗar albarkacin baki da sauran hakkin bil Adam na duniya baki daya, da kuma kawo karshen take hakkin bil Adam."

Bugu da kari, Amurka za ta ci gaba da yin aiki tare da mambobin kasashen duniya don matsa lamba kan sharudan da suka dace don gudanar da zabe cikin 'yanci da adalci a Venezuela.

Har ila yau, Amurka na goyon bayan kokarin rage radadin halin da al'ummar Venezuela ke ciki da kuma kawo karshen wahalhalun da jama’a ke fama da su a Venezuela. Tun daga 2017, Amurka ta ba da fiye da dala biliyan 1.9 na taimakon jin kai, tattalin arziki, ci gaba, da kiwon lafiya don taimakawa Venezuelan daga wadanda suke cikin Venezuela har zuwa waɗanda aka tilastawa tserewa a cikin yankin.

Amurka za ta ci gaba da zama mai ba da shawara ga al'ummar Venezuela yayin da suke kokarin ganin an maido da mulkin dimokradiyya cikin lumana ta hanyar zabe mai inganci da adalci.

XS
SM
MD
LG