Accessibility links

Breaking News

Dole Ne Guetemala Ta Tunkari Matsalar Cin Hanci Da Rashawa


Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken

Amurka ta dakatar da wasu shirye-shiryen hadin gwiwa da Ofishin Babban Lauyan Guatemala don mayar da martani kan korar babban mai shigar da kara na yaki da cin hanci da rashawa.

Babban mai gabatar da kara a Guatemala María Consuelo Porras ta yanke shawarar cire mai gabatar da kara na musamman kan rashin hukuntawa, ko FECI, Cif Juan Francisco Sandoval yana nuna "rashin jajircewa kan bin doka da tsarin shari'a mai zaman kansa da aiwatar da kara," in ji Mataimakiyar Kakakin Ma'aikatar Jiha Jalina Porter.

"A sakamakon haka, ba mu da kwarin gwiwar kan babban lauyan da kuma shawarar da suka yanke - da niyyar yin aiki tare da Gwamnatin Amurka da yakar cin hanci da rashawa da gaskiya."

Mataimakiyar Porter ta jaddada cewa "damuwar da Amurka take nunawa, na tattare ne da abin da ka iya biyo baya kan abin da ya shafi bin tsarin doka da da samar da daidaito a yankin.

Cif Sandoval, wanda aka kora a ranar 23 ga Yuli, ya tsere daga Guatemala a ranar. Masu zanga-zanga a kasar sun yi kira ga Atoni-Janar Porras ta yi murabus.

Amurka ta fayyace wa manyan matakan gwamnatin Guatemala ra'ayinta na cewa yaki da cin hanci da rashawa yana da mahimmanci ga burin karfafa bin tsarin doka, kara habaka karfin tattalin arziki, da magance musabbabin abin da ke mutane suke yin hijira ba bisa ka'ida ba.

Mataimakiyar Porter ta jaddada cewa “Jakadanmu sun isar da sakon ba tare wata kumbaya-kumbiya ba kuma a kwanan nan wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka sun jaddada matsayar kawancen kasashen biyu, ciki har da ziyarar da mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta kai da kuma wacce Shugabar hukumar raya kasashe ta Amurka USAID Samanta Power, da ta shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Homeland Security Alejandro Mayorkas da kuma manzo na musamman Ricardo Zuniga.”

Sakamakon ayyukan babban lauyan, gwamnatin Amurka ta dakatar da wasu ayyukan hadin gwiwa na shirye -shirye tare da Ma'aikatar Jama'a yayin da take gudanar da bitar taimakon da take bayarwa. Amurka tana sa ido sosai ko za ta ga Karin ayyukan da za su lalata tsarin doka ko take 'yancin ganshin fannin shari’ar kasar.

XS
SM
MD
LG