Accessibility links

Breaking News

Dora Alhakin Matsalar Cin Hanci Da Rashawa Akan Shugaban Honduras


Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken

Amurka ta himmatu wajen yaki da ayyukan cin hanci da rashawa da kuma dabbaka tsarin Dimokradiyya, da bin doka a tsakiyar yankin Amurka.

'Yan sandan Honduras sun kama tsohon shugaban kasa Juan Orlando Hernandez a ranar 15 ga watan Fabrairu bayan da Amurka ta nemi a kama shugaban, domin a mika shi saboda zargin hannun da aka same shi da shi a ayyukan safarar miyagun kwayoyi.

Amurka ta himmatu wajen yaki da ayyukan cin hanci da rashawa da kuma dabbaka tsarin Dimokradiyya, da bin doka a tsakiyar yankin Amurka.

“Mun yi amannar cewa wadannan batutuwa su ne ginshikan kyautata makomar yankin Tsakiyar Amurka,” a cewar Sakatare harkokin wajen Amurka Antony Blinken cikin wata sanarwa da ya fitar kwanan nan.

Domin ganin an cimma wannan buri, Amurka ta sanya tsohon shugaban Honduras Juan Orlando Hernandez a jerin sunayen masu dabbaka ayyukan cin hanci da rashawa da yi wa tsarin dimokradiykka zagon kasa, karkashin doka ta 353 ta Amurka.

Hakan na nufin, wadanda sunayensu suka shiga wannan kundi, ba za su samu takardun iznin shiga Amurka ba A ranar 1 ga watan Yulin 2021 aka saka Hernandez a jerin sunayen.

Kamar yadda rahotannin kafafen yada labarai da dama suka ruwaito, Juan Orlando Hernandez ya aikata ayyuka da suka jibinci cin hanci da rashawa da safarar muggan kwayoyi, inda ya yi Amfani da kudaden da ya samu ta wannan hanya wajen yin kamfen dinsa na siyasa

Baya ga haka, shaidu sun ambaci sunan Hernandez a wani bincike da jami’an Amurka suka yi, wadanda suka nuna cewa ya karbi kudaden safarar muggan kwayoyi don yin Amfani da su a kamfen dinsa.

Amurka na ci gaba da amfani da hanyoyinta wajen dabbaka yaki da cin hanci da rashawa da masu kawo tarnaki kan tsaro, da zaman lafiyar a Honduras da Tsakiyar Amurka da sauran duniya.

“Za mu ci gaba da hada kai da jami’an gwamnatin Honduras da mambobin kungiyoyin fararen hula, wadanda suka nuna himma wajen yaki da cin hanci da rashawa da dabbaka tsarin Dimokradiyya da daukan dukkan matakan gano kaura da mutane ke yi daga yankin.” Blinken ya ce

Amurka za ta ci gaba da nuna goyon bayan Honduras yayin da take kokarin ganin ta amfana da turakun Dimokradiyya, da samar da damammaki daidai-wadaidai da kuma samar da makomar mai kyau da suke muradin samarwa kansu da iyalansu.

XS
SM
MD
LG