Accessibility links

Breaking News

Karrama Jaruman 'Yan 'Jarida (• Grace Alheri AbduHONORING BRAVE JOURNALISTS)


Kwanan nan Shugabar Hukumar Kula da Cigaban Ƙasashen Duniya ta Amurka, Samantha Power ta taya waɗanda suka lashe lambar yabo ta Kurt Schork a aikin jarida na duniya na wannan shekara. Kyautar ta karrama jaruman ‘yan jarida, wadanda galibinsu ba a ma san da sub a, saboda rahotanninsu kan rikice-rikice, cin hanci da rashawa, da rashin adalci .

Wadanda suka lashe kyautar a bana sun hada da wani Ba’amurke dan asalin kasar Iran, Jason Motlagh, dan jaridar Brazil Rafael Soares, da Khabat Abbas daga Syria.

Yanzu a cikin shekarar ta 20, an ba da lambar yabo ta Kurt Schork a aikin jarida na kasa da kasa don girmama dan jaridar Amurka mai zaman kansa Kurt Schork, wanda aka kashe a Saliyo yayin da yake aiki a kamfanin dillancin labarai na Reuters a shekara ta 2000.

Ganin mahimmancin aikin jarida mai 'yanci, USAID na taimaka wa 'yan jarida a kasashe fiye da 30 da kariya da taimakon shari'a ga wadanda ke fuskantar barazana. "Shirye-shiryen mu," in ji shugabar Samantha Power, "taimakawa wajen inganta aikin jarida mai zaman kansa, aiki kamar yadda muka sani na da muhimanci ga al'ummomin lafiya da tattalin arziki masu wadata."

Sau da yawa ana sanya 'yan jarida cikin babban haɗari saboda kawai faɗin gaskiya da sanar da jama'a, in ji Power:

“Hakika wannan gaskiya ne game da ’yan jarida da muke darajanta waɗanda suka ba da rahoton yaƙin Afganistan, kisan gilla da aka yi a Brazil, da kisan gilla a Siriya, sa yara aiki a Pakistan, da kuma tsarin shari’ar manyan laifuka a Najeriya.

Ayyukan da suka yi sun fallasa gaskiya game da yaƙi da rikice-rikice, tare da fallasa cin zarafin ɗan adam, wariya, da cin hanci da rashawa. Kuma sadaukarwasu na fadin gaskiya ga masu mulki ya zo a wani muhimmin lokaci na aikin jarida.”

XS
SM
MD
LG