Accessibility links

Breaking News

Nasarar Cimma Yarjejeniyar Kare Teku


Matsalolin Dumamar Yanayi a Teku
Matsalolin Dumamar Yanayi a Teku

Bayan shafe shekara da shekaru ana tattaunawa, kasashe 190 mambobin Majalisar Dinkin Duniya sun zana daftarin kundin kare manyan tekuna – da sashin manyan tekuna da ba su cikin kasashe. Tattaunawa kan yarjejeniyar da aka cimma biyo bayan tarukan gwamnatocin kasashe kan nau’ukan halittun ruwa da kuma albarkatun ruwa da ke yankunan ruwa da ba mallamar wata kasa ba ne, BBNJ, ko kuma Yarjejeniyar Manyan Teku, da aka fara tun a 2018, wadda aka biyo bayanta da wasu ayyukan da aka kwashe shekaru gwammai ana yi a Kwamitin Shirye Shirye da kuma kwamitin aiki da cikawa.

Dumamar yanayi a teku
Dumamar yanayi a teku

A halin yanzu, kashi 1.2 cikin 100 ne kawai na wannan yankunan ruwayen ke karkashin cikakkiyar kulawa da samun kariya daga illar da gurbata muhalli, yawan su, jigilar kan ruwa, da kuma hakar ma’adinai a can karkashin teku. Da zarar kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya su ka rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar, za ta zama wani muhimmin fanni na cimma burin da ake da shi na karewa ko ceto a kalla kashi 30 cikin 100 na manyan tekuna zuwa shekara ta 2030, abin da ake kira shirin 30X30. Wannan shirin, wanda wani mizani ne da kimiyya ke nuna cewa ya na da matukar muhimmanci wajen shawo kan matsalar dumamar yanayi da kuma kare tarayyar halittu, na da zummar samar da yanayi mai kyau ga kowa; da bayar da gudunmawa ga kokarin da ma’abuta yankunan kasa ke yi na kare muhalli; da taimakawa wajen daidaita yanayi, da kuma tabbatar da samun alaka tsakanin siffar yankin kasa da kuma dabbobin daji da ke zama ciki.

Babban burin yarjejeniyar BBNJ shi ne kare halittun ruwa. Bisa ga bayanin Kungiyar Kasa da Kasa ta Kare Komai Yadda ya ke, kusan kashi 10 cikin 100 na nau’ukan halittun ruwa da ke duniyar nan na fuskantar barazanar shudewa. “Zaman tarayya na halittu na dusashewa cikin wani irin sauri mai matukar hadari,” a cewar Mataimakiyar Sakataren Harkokin Manyan Tekuna da Muhallin Kasa da Kasa da Kimiyyar, Monica Medina.

Ta ce, “Kare a kalla kashi 30 ciki 100 na duniya – da doron kasar ciki, da yankunan ruwan ciki, da kuma manyan tekuna – na da muhimmanci gaya wajen taimaka ma abubuwan halitta su iya tallafa ma al’umma, tattalin arziki, da kuma duniyarmu.”

Sauyin yanayi wani babban musabbabin dasashewar rayuwar halittun ruwa ne. Karuwar zafin teku, canjin sinadaran cikin ruwa, da kuma sauran abubuwan da iska mai gurbata muhalli ke haddasawa da dada sawa zama cikin ruwa na wuya ga wasu nau’ukan halittu da dama. Aiwatar da tsare tsaren kare rayuwar halittun ruwa na da matukar muhimmanci wajen magance barazanar da muhalli ke fuskanta, shudewar zaman tarayyar halittu, da gurbatar yanayi, kuma wannan Yarjejeniyar Kare Manyan Tekuna za ta taimaka ma na mu cimma wannan burin.

“Akwai alaka ta kud da kud tsakanin matsalolin da manyan tekuna ke fuskanta da wadanda yanayi ke fuskanta,” a cewar Manzon Musamman na Shugaban Amurka kan Batutuwan Sauyin Yanayi, John Kerry.

A cewar Manzon Musamman Kerry, Yarjejeniyar Manyan Tekuna na jan hankalin duniya zuwa ga nau’ukan barazana da tekunan duniya ke fuskanta da kuma hobbasar da ya kama a yi don magance matsalar yanayi ta yadda za a kare ko ceto sassa masu yawa na manyan tekuna zuwa sekara ta 2030.

Anncr: Wannan shi ne Sharhin Muryar Amurka, mai bayyana ra’ayin gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG