Gwamnatin Rasha ta janye daga shirin fitar da hatsi da aka fara ta hanyar Bahr Al Aswad, lamarin da kai ya jefa tsarin samar da abinci a sassan duniya cikin mawuyacin hali.
Shirin fitar da hatsin, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta samar, na kunshe ne da aikawa da hatsi daga wasu muhimman tashoshin jiragen ruwa uku a Ukraine.
Wakilai daga Ukraine, Rasha, Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a watan Yuli, wacce ake sa ran za a sabunta a wannan wata na Nuwamba, matakin da ya taimaka wajen magance matsalar karancin abinci a sassan duniya.
Jirgin ruwan farko da ya bar tashar jirgin ruwa ta Odesa a ranar 1 ga watan Agusta na makare ne da sama da tan 26,000 na hatsi.
Tun kuma daga lokacin, kusan jirage 400 sun fitar da kayan da tan dinsu ya kai miliyan 9.2, da suka hada da masara, alkama, waken soya da sauransu.
Ita dai Ukraine ta kasance kasar da ta fi kowacce noman hatsi iri-iri a cewar ma’aikatar noma ta Amurka. Sannan it ace kasa ta bakwai da a jerin kasashen da suka yin noman alkama.
A cewar Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, “Amurka na takaicin janyewar da Rasha ta yi a wannan shiri na samar da hatsi da majalisar dinkin duniya ta samar.
“Shirin ya samu nasara wajen kai wag a mutane da suke matukar bukatar abinci da ke fitowa daga Ukraine ta Bahr Al Aswad zuwa kasuwar duniya.” In ji Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield.
“Shirin ya taimaka waje rage farashin kayan abinci a duniya ya kuma tabbata kayan hatsi da hukumar samar da abinci ta duniya ta sayo, sun kai ga mabukata a Yemen, Ethiopia, Afghanistan da Somalia.”
“Duk wani yunkuri da Rasha ta yi na kawo cikas wajen fitar da hatsin, abu ne da ke nuni da cewa, mutane iyalai a sassan duniya za su sayi abinci da tsada ko kuma su zauna da yunwa.” In ji Sakatare Blinken.
“Janyewa daga shirin, Rasha na amfani da abinci a matsayin makami a yakin da ta fara, lamarin da yake tasiri kai-tsaye akan kasashen marasa karfi da ksuwar samar da abinci a duniya, lamarin da ke kara dagula al’amura.
“Muna kira ga gwamnatin Rasha da ta dawo cikin wannan shiri,” in ji Sakatare Blinken, “domin a bi tsarin da aka shata, a kuma yi aiki don a tabbatar mutane a sassan duniya na ci gaba da samun mafita.