Accessibility links

Breaking News

Yaki Da Masu Safarar Miyagun Kwayoyi


Muguwar kwayar nan ta Fentanyl, wadda aka yi safararta ta kan iyakar kudancin Amurka, ita ce ummul aba’isin fiye da kashi 63 cikin 100 na yawan mace mace wajen 96,779 sanadiyyar miyagun kwayoyi a Amurka tsakanin Maris 2020 da 2021. Domin dakile guguwar miyagun kwayoyi da ke shigowa Amurka, Amurka ta dukufa wajen inganta matakan ta ke daukawa don ganin an rage bukatar shan kwayoyin, tare kuma da dakile safararsu da manyan laifukan da akan ketare kan iyakoki a haddasa a fadin duniya, musamman ma Mexico.

Kwanan nan, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da tayin bayar da tukwicin dala miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayanin da ya kai ga kamawa ko hukunta wasu masu safarar miyagun kwayoyi su hudu da ke aika aikarsu a jihohin Chihuahua da Sinaloa na Mexico. Aureliano Guzman-Loera, ɗan'uwan tsohon shugaban kungiyar masu safarar muggan kwayoyi ta Sinaloa Cartel, Joaquin Guzman-Loera, da 'yan'uwan Ruperto Salgueiro-Nevarez, Jose Salgueiro-Nevarez, da Heriberto Salgueiro-Nevarez duk suna aika aikarsu a ƙarƙashin kungiyar Sinaloa Cartel.

Ana tuhumar Aureliano Guzman-Loera da ’yan’uwan Salgueiro-Nevarez saboda keta dokokin miyagun ƙwayoyi na Amurka, gami da dokokin ƙasashen duniya don rarraba tabar wiwi, hodar koken, methamphetamine, da fentanyl.

Tayin wannan kyautar ya karfafa sanarwar Ma'aikatar Shari'a ta tuhumar Aureliano Guzman-Loera da 'yan'uwan Salgueiro-Nevarez guda uku saboda keta dokokin fataucin miyagun kwayoyi na duniya.

Ana bayar da wannan tukwicin ne a ƙarƙashin Shirin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na bayar da kyautattuka don dakile miyagun kwayoyi (Narcotics Rewards Program). Masu aikata laifuka sama da 75 da manyan masu safarar miyagun kwayoyi ne aka gurfanar da su gaban kuliya a karkashin shirin na Narcotics Rewards Program and the Transnational Organized Crime Rewards Program tun daga shekarar 1986. Ma'aikatar ta biya fiye da dala miliyan 135 a matsayin tukwici ga duk wanda ya ba da labarin da ya kai ga kama mutane.

Ofishin sa ido kan miyagun kwayoyi da Harkokin Jami’an Tsaro ke kula da shirin na biyan tukwici tare da hadin gwiwar Hukumar Tabbatar da Aiwatar da kokokin Dakile Kwayoyi, da FBI, Hukumar Shigi da Fici ta Amurka da sauran cibiyoyin Amurka. Wannan matakin nanu yadda Ma’aikatar ta Harkokin Waje ta dukufa wajen goyon bayan jami’an tsaro a kokarin ganin an gurfanar da masu aikata laifuka na kasa da kasa.

XS
SM
MD
LG