Syria Na Ci Gaba Da Gazawa Wajen Mutunta Yarjejeniyar Makamai Masu Guba Da Aka Kulla

Bashar al-Assad yana jawabi a wani taro da aka yi a Damascus, a watan Yulin 17, 2021.

Bashar al-Assad yana jawabi a wani taro da aka yi a Damascus, a watan Yulin 17, 2021.

Jakadiya Thomas-Greenfield ta lura cewa kawayen gwamnatin Assad, ciki har da Rasha, "sun yi matukar yunkurin toshe duk wata hanyar bin ba'asi." 

Shekaru takwas kenan da gwamnatin Assad ta kai harin makaman guba kan 'yan kasarta a yankin Ghouta da ke bayan garin Damascus wanda ya kashe sama da ‘yan Siriya 1,400, wadanda daruruwansu yara ne. Dubban mutane kuma sun jikkata. Wannan ba shi ne karon farko ba; kuma abin takaici, ba shi ne zai zama na ƙarshe ba da gwamnatin za ta kai wa mutanenta harin makamai masu guba, to amma tsananin harin da aka kai Ghouta ya girgiza duniya.

A wata na biye, biyo bayan yinkurowa da ƙasashen duniya suka yi, gwamnatin Siriya ta amince da Yarjejeniyar Makamai Masu guba, ta kuma amince ta kawar da makamai masu guba da ta tara da kuma bayar da hadin kai ga Kungiyar Yaki Da Makamai Masu Guba (OPCW, a takaice) a aikace aikacenta na saka ido da bincike.

To amma gwamnatin Assad ta kasa cika alkawuran da ta dauka. Ko bayan kawar da tarin makamai masu guba da Siriya ta bayyana su, gwamnatin ta Siriya ta sha yin amfani da makamai masu guba kan mutanen ta, kuma, kamar yadda Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield ta ce a wani taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan, Siriya ta yi kokarin kauce ma fuskantar sakamako ta hanyar kawo cikas ga bincike mai zaman kansa da rashin bayar da hadin kai ga OPCW.

Amurka na matukar goyon bayan aikin OPCW da hukumomin bincikenta na ba sani ba sabo. Ambasada Thomas-Greenfield ta yi nuni da cewa tawagar Bincike da Tabbatar da Al'amura ta Kungiyar OPCW ta danganta hare-haren makamai masu guba guda hudu a Siriya da gwamnatin Assad. Waɗannan abubuwan sun haɗa da hare-haren makamai masu guba guda huɗu waɗanda a baya aka danganta su ga gwamnatin Assad ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar ta OPCW.

Jakadiya Thomas-Greenfield ta lura cewa kawayen gwamnatin Assad, ciki har da Rasha, "sun yi matukar yunkurin toshe duk wata hanyar bin ba'asi." Rawar da Rasha ta taka wajen bai wa gwamnatin Assad karfin gwiwa"na da hadari," in ji ta. "Ba za a lamunta da maimaitawa da kuma ci gaba da gazawar gwamnatin Assad wajen bin ka'idodin da ke ƙarƙashin dokar ƙasa da ƙasa ba."

Jakadiya Thomas-Greenfield ta lura cewa Kwamitin Tsaro ya yanke shawara, idan ba a bi ka'idojin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na 2118 ba, wanda baya ga sauran wasu abubuwa, ya hana gwamnatin Siriya amfani da makamai masu guba, don sanya matakan a karkashin Babi na Bakwai na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya. .

Ta kara da cewa "A yanzu muna da kwararan abubuwan da dama na kafa shaida kan cewa gwamnatin Assad ta yi ta saba ma yarjejeniyar." “Yanzu ne lokacin da za mu tabbatar da aiwatar da shawarar wannan Majalisar. Ba tare da la’akari da ta’asar da aka yi wa mutanen Siriya ba, zaman lafiya mai dorewa a Siriya zai ci gaba da kasancewa abu mai wuya. ”